Ku bude makarantuku - Gwamnatin tarayya ta baiwa jihohi dama

Ku bude makarantuku - Gwamnatin tarayya ta baiwa jihohi dama

- Ma'aikatar ilimin tarayya ta ce gwamnatocin jihohi ne zasu yanke lokacin da zasu bude makarantun dake karkashinsu

- Chukwuemeka Nwajiuba, karamin ministan Ilimi ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai

- Ministan ya kindaya ka'idojin bude makarantu kuma an baiwa dukkan jihohin Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ce ta baiwa jihohi daman bude makarantu kuma su ke da zabin lokacin da zasu bude.

Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya bayyana hakan ranar Alhamis, 17 ga Satumba, yayin amsa tambayoyi a hira da manema labaran kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da COVID-19 kamar yadda aka saba.

Ministan ya ce tuni gwamnatin tarayya ta baiwa jihohi daman bude makarantunsu.

Amma Nwajuiba ya ce wajibi ne gwamnatocin jihohi su bi sharrudan kare dalibai da cutar COVID-19 da gwamnatin tarayya ta gindaya.

Ya ce gwamnatin tarayya ta yi na ta aikin na samar da takardan sharrudan saboda haka hakki bude makarantu ya rataya kan jihohi.

Tuni Jihohi da dama sun sanar da ranakun bude makarantunsu.

Daga cikin jihohin da suka sanar da ranar budewa akwai jihar Legas, Oyo, Delta, Bayelsa, Ogun, Ekiti, da sauransu.

DUBA NAN Hukumar raya birnin tarayya ta fara rusa gidajen karuwai a Abuja

Ku bude makarantuku - Gwamnatin tarayya ta baiwa jihohi dama
Ku bude makarantuku - Gwamnatin tarayya ta baiwa jihohi dama
Source: Twitter

KARANTA NAN:Auri saki: Auren Fani Kayode na hudu ya mutu sakamakon dukan matarsa

A bangare guda, Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa an sallami mutane 3442 dake fama da cutar Korona a birnin tarayya Abuja, jihar Kwara da wasu jihohin Najeriya a yau kadai.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:30 na daren ranar Laraba 16 ga Satumba, shekarar 2020.

Hukumar ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 126 a fadin Najeriya.

Jawabin hukumar yace: "Warakan da muka samu yau mutane 2,967 a birnin tarayya da 103 a jihar Kwara da aka yiwa jinya cikin gida bisa sharrudan da hukumar ta gindaya."

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 126 da suka fito daga jihohin Najeriya.

Kawo yanzu, jimillan mutane 56,604 suka kamu da cutar a Najeriya, yayinda 47,872 suka warke, 1,091 sun mutu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel