'Kusohin gwamnati ke bawa ƴan bindiga kariya - Kungiyoyin Arewa

'Kusohin gwamnati ke bawa ƴan bindiga kariya - Kungiyoyin Arewa

- Haɗakar wasu kungiyoyin siyasa da cigaba al'umma a arewa, CNG, ta buƙaci Shugaba Buhari ya yi tankaɗe da rairaya

- Ƙungiyoyin sun yi iƙirarin cewa akwai wasu mutane masu ƙarfin iko a gwamantin Buhari da ke ɗaure wa ƴan bindiga gindi

- Ƙungiyoyin sun yi wannan jawabin ne game da zargin da suke yi na cewa an saki wasu da ake zargin ƴan bindiga ne a Zamfara ba tare da bin ƙa'ida ba

Haɗakar ƙungiyoyin siyasa da cigaba al'umma ƙarƙashin inuwar Coalition of Northern Groups, CNG, ta faɗa wa Shugaba Muhammadu Buhari ya bincika mutanen da ke kusa da shi domin wasu daga cikinsu na ɗaure ƴan bindiga gindi.

A yayin ta kungiyar ke kira a gudanar da sahihin bincike a kan sakin wasu manyan ƴan bindiga 18 a Zamfara ciki har da Abu Ɗan-Tabawa, ƙungiyar ta ce wai wasu masu faɗa a ji a suna kare wadanda ke kawo cikas ga binciken kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Wasu manya a gwamnati ke daure wa yan bindiga gindi – Hadakar Arewa
Wasu manya a gwamnati ke daure wa yan bindiga gindi – Hadakar Arewa. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Bill Gates: Abinda Najeriya za ta yi don tsamo 'yan kasarta daga ƙangin talauci

Kakakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman yayin taron manema labarai a ranar Laraba a Abuja ya ce an saki Ɗantabawa da aka ce shi ya tarwatsa zaɓen raba gardama na Majalisar Wakilai 'saboda matsin lamba da aka yi wa hukumomin tsaro'.

Ya ce, "Ba za mu amince a riƙa kare ƴan bindiga da masu aiki tare da su ba. Muna kira a gudanar da sahihin bincike a gano manyan mutanen da ke hana a hukunta ƴan bindiga da masu aiki da su a Zamfara da sauran wurare a arewa.

KU KARANTA: Hotuna: Wani mutum ya auri surukarsa bayan rabuwa da matarsa

"Muna kira a gudanar da cikakken bincike don gano abinda yasa aka saki Ɗantabawa da wasu da ake zargi ba tare da bin ƙa'ida ba. Muna kira ga hukumomin tsaro su dena nuna banbanci wurin magance sauran matsalolin da suka yi saura a Katsina da wasu wurare da aka fara samun sauƙi.

"Muna bada shawarar a fara irin wannan binciken a Niger da Nasarawa a yanzu ƴan bindiga suka fara adabar mutane da hari da garkuwa."

A wani labarin, Jama'ar kauyen Unguwar Gambo da ke karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina sun kashe wasu 'yan bindiga wadanda da ba a san yawansu ba.

Wasu mazauna yankin sun sanar da jaridar Daily Trust cewa, lamarin ya auku a ranar Lahadi yayin da daya daga cikin wadanda ake zargin dan bindiga ne ya bayyana sunan wadanda suke hada kai wurin aika-aikar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel