Auri saki: Auren Fani Kayode na hudu ya mutu sakamakon dukan matarsa

Auri saki: Auren Fani Kayode na hudu ya mutu sakamakon dukan matarsa

- Bayan rikici da yan jaridar Najeriya kwanakin baya, sunan Fani Kayode ya sake dawowa kafafen sada zumunta

- Wannan karon ana zarginsa da cin zarafin matarsa da ta haifa masa 'yara maza hudu

- Precious ce mata ta hudun da Fani Kayode ya aura a rayuwarsa

Tsohon ministan sufurin saman Najeriya, Femi Fani-Kayode da tsohuwar matarsa, Precious Chikwendu, sun rabu.

Wannan shine aurensa na hudu da zai mutu.

Wani dan gidan ya bayyanawa PREMIUM TIMES cewa auren ya mutu ne sakamakon rashin lafiya da matar ke fama da shi tun lokacin da sukayi aure.

Amma Sahara Reporters ta ce ta tattaro cewa matar ta gudu daga gidan ne saboda yawan dukanta da yake yi.

Fani-Kayode, wanda rabu da mata uku da ya aura a baya ya hadu da Precious ne kuma ta haifa masa yara hudu.

Tana tuhumarshi da laifin neman mata.

KU KARANTA: Ka sauka daga mulki idan ba zaka iya bamu tsaro ba - Babban Limamin jami'ar Abuja ya caccaki Buhari

Majiyar Sahara Reporters sun bayyana cewa tsohon ministan yana bugun Precious tun shekarar da suka yi aure -- irin abinda ya yiwa matansa na baya.

Rahoton ya bayyana cewa Fani Kayode ya umurci Precious ta zubar da cikin da take dauke da shi saboda bai yarda cikinsa bane.

Amma Precious tayi banza da shi kuma hakan yayi sanadiyar duka iri-iri saboda ta ki bin umurninsa.

Matar farko da Fani Kayode ya aura, Saratu Attah, ta rabu da shi ne sakamakon yawan bugun da yake mata.

Hakazalika matarsa ta biyu, Yemisi Odesanya, diyar wani Alkali, wacce ta zargeshi da laifin rashin kula da yaranta.

Auri saki: Auren Fani Kayode na hudu ya mutu sakamakon dukan matarsa
Auri saki: Auren Fani Kayode na hudu ya mutu sakamakon dukan matarsa
Asali: Instagram

KU KARANTA: Hukumar raya birnin tarayya ta fara rusa gidajen karuwai a Abuja

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel