Shehu Sani ya caccaki Masari a kan bai wa tubabbun 'yan bindiga gidaje da gonaki da zai yi

Shehu Sani ya caccaki Masari a kan bai wa tubabbun 'yan bindiga gidaje da gonaki da zai yi

- Sanata Shehu Sani, ya caccaki gwamnan jihar Katsina, Aminu Belleo Masari a kan tagomashin da yake yunkurin gwangwaje 'yan bindiga da shi

- Gwamna Masari ya ce zai bai wa tubabbun 'yan bindiga gidaje, gonaki da shagunan kasuwa matukar za su yada makamai

- Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa hakan hanya ce ta kara wa 'yan bindiga kwarin guiwa tare da sa wa wasu son fadawa harkar

Tsohon dan majalisar dattawa wanda ya wakilci jihar Kaduna ta tsakiya a majalisa karo ta takwas, Sanata Shehu Sani, ya caccaki Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina a kan yunkurin gwangwaje tubabbun 'yan bindiga da gonaki da gidaje.

Idan za mu tuna, Masari a ranar Laraba ya fara bayanin yadda za a bi da 'yan bindiga ta hanyar basu gidaje, shagunan kasuwanni da gonaki ga duk wanda zai ajiye makamai domin tabbatar da wanzuwar tsaro a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa, ya ce gwamnatin jihar ta kammala shirinta na karbar tubabbun 'yan bindiga kuma za ta basu muhalli.

"Wannan yana daga cikin shirin gwamnatin na gyara dajin Rugu kuma ta bai wa tubabbun 'yan bindigar. An kafa kwamiti domin samar musu da ababen more rayuwa.

"Wasu daga cikin yankunan sun hada da dajin yankin Yantumaki da Maidabino da kuma dajin Sabwa da Faskari," Inuwa yace.

A yayin martani ta shafinsa na Twitter, Sanata Sani, ya ce wannan kawai hanya ce ta gwangwaje masu laifi.

Kamar yadda yace, wannan karamcin zai kara fadada laifuka tare da kara bai wa wasu kwarin guiwa.

"Gwamnatin jihar Katsina tana kokarin bai wa 'yan bindiga gonaki, shagunan kasuwa da gidaje wanda hakan hanya ce ta karrama 'yan ta'adda.

"Hakan kuwa zai kara musu kardin guiwa tare da bai wa wasu sha'awar shiga harkar. Zai kara tsananta matsalar tsaro a yankin arewa," Sani ya wallafa.

KU KARANTA: Tarihi ya kafu, jirgin kasa ya tashi daga Legas zuwa Ibadan (Bidiyo)

Shehu Sani ya caccaki Masari a kan bai wa tubabbun 'yan bindiga gidaje da gonaki da zai yi
Shehu Sani ya caccaki Masari a kan bai wa tubabbun 'yan bindiga gidaje da gonaki da zai yi. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: Babu dadewa za mu samu man fetur a farashi mai sauki - FG

A wani labari na daban, a kokarin ganin bayan 'yan bindiga da suka addabi yankin arewa maso yamma, rundunar Operation Sahel Sanity, ta ceto mutum 32 da aka yi garkuwa da su.

Ta cafke 'yan bindiga 26, masu hada kai da su, samar musu da makami da miyagun kwayoyi bayan musayar wuta da suka yi.

A wannan musayar wutar, biyu daga cikin 'yan bindigar sun rasa rayukansu, Vanguard ta wallafa. Mukaddashin daraktan yada labarai na rundunar sojin, Birgediya Janar Benard Onyeuko, wanda ya fitar da sanarwar, ya ce an samu shanun sata har 150 bayan artabun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel