Abinda yasa muka kama jigon jam'iyyar APC a Zamfara - 'Yan sanda

Abinda yasa muka kama jigon jam'iyyar APC a Zamfara - 'Yan sanda

- Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta yi karin haske game da kama shugaba a jam'iyyar APC na Zamfara, Dan-Tabawa da wasu mutum 17

- Kwamishinan 'yan sandan jihar, Usman Nagogo ya ce sun samu bayanan sirri kan cewa wasu na taro da tubabbun 'yan bindiga da nufin hure musu kunne su koma daji shi yasa suka kai sumamen

- Nagogo ya musanta cewa kamen na da alaka da siyasa inda ya ce kawai rundunar ta dauki mataki ne domin dakile yiwuwar wasu su hure wa 'yan bindigan kunne

Rundunar 'yan sandar jihar Zamfara a ranar Alhamis ta ce ta kama jigon jam'iyyar APC a jihar, Habu Dan-Tabawa ne bayan ya yi taro da tubabbun 'yan bindiga a gidansa da ke Gusau a ranar Asabar.

Tuni dai an sako Mista Dan-Tabawa, shugaba a jam'iyyar ta APC a Zamfara tare da wasu mutane 17 da aka kama daga wurin taron. Amma ya ce kama shi na da alaka da siyasa.

Abinda yasa muka dan jam'iyyar APC a Zamfara - 'Yan sanda
Abinda yasa muka dan jam'iyyar APC a Zamfara - 'Yan sanda. Hoto daga Premium Times
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Fursunoni 200 sun tsere daga gidan yari tsirara a Uganda

Amma kwamishinan 'yan sandan jihar, Usman Nagogo, yayin taron manema labarai a Gusau, a ranar Alhamis ya ce an sanar da rundunar cewa wasu mutane suna taro da tubabbun 'yan bindiga don su hure musu kunne su fara kai hare-hare.

"Babu wata hukumar tsaro da za ta kalmashe hannu ta jira har sai an fara kai wa mutane hari kafin ta dauki mataki," a cewar kwamishinan 'yan sandan.

"Don haka, bayannan sirri ne da kokarin kare afkuwar fitina a jihar yasa aka kama Alhaji Habu Moh'd Dan-Tabawa da sauran mutanen 17," in ji Mista Nagogo.

Kwamishinan ya ce wasu miyagu sun kai hari hedkwatan rundunar yan sandan a ranar Lahadi, kwana daya bayan kama 'yan siyasan.

Ya ce an kai harin ne da nufin lalata hujojjin da 'yan sandan suka samu domin kawo cikas ga binciken da rundunar ke yi a kan mutanen da aka kama.

KU KARANTA: Bill Gates: Abinda Najeriya za ta yi don tsamo 'yan kasarta daga ƙangin talauci

Ya kara da cewa, "Ina gargadin duk wasu masu irin wannan halin su sani cewa za su gamu da fushin hukuma dai-dai yadda doka ta tanada."

A bangarensa, Dan-Tabawa ya ce zargin da aka masa ba gaskiya bane kuma an yi hakan ne domin bata masa suna.

A taron manema labarai da ya yi a ranar Talata, ya ce ya shigo ne daga Kaduna domin jajantawa wadanda ambaliyar ruwa ya shafa a garinsu amma kimanin karfe 9 na dare 'yan sanda suka afka gidansa suka kama shi da abokansa 16.

A cewarsa wadanda aka kama sun hada da sakatarorin dindindin a jihar da mambobin PDP da kan kawo masa ziyara idan ya zo gari.

A wani rahoton, kun ji cewa wani dan kasuwa, Iga Bale, a ranar Laraba ya roki kotun gargajiya da ke Nyanya Abuja ta raba aurensa da matarsa Liza a kan cewa ta rantse sai ta gallaza masa ta mayar da shi tamkar mabaraci.

Bale ya roki wannan alfarman daga hannun kotu ne cikin takardar neman raba aure da ya shigar a kotun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel