Hukumar yan sanda ta tabbatar da harin da aka kaiwa jami'anta a Sokoto (Hotuna)

Hukumar yan sanda ta tabbatar da harin da aka kaiwa jami'anta a Sokoto (Hotuna)

- Duk da sulhun da gwamnatin Sokoto keyi da yan bindiga, da alamun har yanzu akwai sauran aiki

- Yan bindiga sun kaiwa yan sanda farmaki a ofishinsu dake jihar Sokoto

- Bayan kisan jami'an yan sanda biyu da sukayi, yan bindigan sun yi awon gaba da matan aure

Hukumar yan sanda a jihar Sokoto ta tabbatar da harin da ake zargin yan bindiga suka kaiwa jami'anta dake ofishin Gidan Madi, karamar hukumar Tangaza ta jihar.

Kakakin hukumar yan sanda jihar, ASP Mohammed Sadiq Abubakar, ya ce harin ya auku ne a daren Laraba amma har yanzu ba'a samu cikakken bayanin abinda ya auku ba, TVC ta ruwaito.

Kaakin yan sandan ya yi kira da al'umma su saurari sakamakon binciken da kwamishanan yan sandan jihar, Sani Kaoje, ya kaddamar.

Wasu majiyoyi a karamar hukumar sun bayyanawa wakilin TVC cewa an kashe jami'an yan sanda biyu a harin kuma ana kyautata zaton daya daga cikinsu DPO ne.

Hukumar yan sanda ta tabbatar da harin da aka kaiwa jami'anta a Sokoto
Hukumar yan sanda ta tabbatar da harin da aka kaiwa jami'anta a Sokoto
Source: Twitter

Hukumar yan sanda ta tabbatar da harin da aka kaiwa jami'anta a Sokoto
Hukumar yan sanda ta tabbatar da harin da aka kaiwa jami'anta a Sokoto
Source: Twitter

DUBA NAN: Ana shirin shigo da kaji masu dauke da cutar Korona Najeriya - Hameed Ali, CG Kwastam

Hukumar yan sanda ta tabbatar da harin da aka kaiwa jami'anta a Sokoto
Hukumar yan sanda ta tabbatar da harin da aka kaiwa jami'anta a Sokoto
Source: Twitter

Wani ganau da ya bukaci a sakaya sunan sa, ya bayyana cewa ya ji karar harbe harbe a tsakiyar dare, lamarin da ya tilastasu tashi daga barci.

KARANTA WANNAN: Yan APC a Edo na karban katin zaben mata suna basu Atamfa (Bidiyo)

Bayan 'yan bindigar sun kashe DPO, sun kuma shiga cikin garin Gidan Madi, inda suka yi awon gaba da wasu mata, kamar yadda mazauna garin suka tabbatar.

Haka zalika, rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun yi awon gaba da makamai, musamman bindiga kirar AK47.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel