Bill Gates: Abinda Najeriya za ta yi don tsamo 'yan kasarta daga ƙangin talauci

Bill Gates: Abinda Najeriya za ta yi don tsamo 'yan kasarta daga ƙangin talauci

- Attajirin duniya kuma daga cikin wanda suka kafa Microsoft, Bill Gates ya magantu a kan hanyoyin da Najeriya za ta tsamo yan kasarta daga talauci

- Attajirin dan kasuwan ya lissafa abubuwa da suka hada da kiwon lafiya, ilimi, samar da abinci da kuma kara haraji

- Mista Gates ya ce Najeriya tana cikin kasashe mafi saukin haraji kuma gwamnati ba za ta iya samun kudaden yin ayyuka ba idan babu haraji

Fitaccen mai kudin duniya kamu mai tallafawa al'umma Bill Gates ya yi magana game da matakan da Najeriya za ta iya dauka domin tsamo 'yan kasar daga talauci.

An yi kisayin cewa a kalla 'yan Najeriya miliyan 82.9 suke rayuwa cikin talauci, hakan yasa aka yi wa Najeriya lakabi "babban birnin talauci na duniya".

Bill Gates: Abinda Najeriya za ta yi don tsamu 'yan kasarta daga talauci
Bill Gates: Abinda Najeriya za ta yi don tsamu 'yan kasarta daga talauci. Hoto daga Vanguard/The Nation
Source: Twitter

A wata hirar da The Cable ta yi da shi, an tambayi attajirin dan kasuwan hanyoyin da Najeriya za ta bi domin tsamo mutanen ta daga talauci, ya lissafa inganta kiwon lafiya, ingantaccen ilimi, karin haraji da sauransu.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe mahaifi, sun yi awon gaba da ɗansa a Katsina

Ya ce: "Ka san akwai hanyoyi mabanbanta da za a iya rage talauci. Wanda ya fi muhimmanci shine lafiya; idan yara suna girma cikin koshin lafiya za su iya samun ilimi su girma su bada gudunmawa a kasa, idan ka basu abinci mai kyau za su kara kuzari da hazaka."

A gani na kiwon lafiya ya dace Najeriya ta fi mayar da hankali a kai; sannan sai ilimi mai inganci, sai gine-gine da zaman lafiya da bangaren shari'a.

Mista Gates ya cigaba da cewa, "Yan Najeriya ba su yarda cewa ana amfani da kudin harajin da suke biya ta yadda ya dace ba saboda haka ya kamata a samu yarda tsakanin gwamnati da al'umma sannan a kara haraji.

KU KARANTA: Bidiyo: Sojoji sun tarwatsa mafakan shugabannin 'yan bindiga Damina da Sani Mochoko a dajin Kuyambana a Zamfara

Najeriya na cikin kasashen mafi saukin haraji a duniya saboda haka zai yi wahala gwamnati ta inganta ilimi da gine gine.

Ya kamata a nuna wa mutane cewa ana kashe kudin harajinsu ta yadda ya dace. Hanya guda na yin hakan shine samar da magunguna, tabbatar da ma'aikatan lafiya na zuwa aiki a kuma fayyace abinda ake son cimma hakan zai sa mutane su ga ana ceto rayuwa.

Inda muka fi kwarewa shine bangaren lafiya saboda muhimmancinsa amma an bar shi a baya, musamman a arewacin kasar domin an bar su baya har wasu kasashen da ba su kai Najeriya kudi ba sun fi su.

A wani labari daban, kun ji cewa wani dan kasuwa, Iga Bale, a ranar Laraba ya roki kotun gargajiya da ke Nyanya Abuja ta raba aurensa da matarsa Liza a kan cewa ta rantse sai ta gallaza masa ta mayar da shi tamkar mabaraci.

Bale ya roki wannan alfarman daga hannun kotu ne cikin takardar neman raba aure da ya shigar a kotun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel