Nigeria@60: Babu kasar da ta kai Najeriya cigaba a nahiyar Afrika - Buhari

Nigeria@60: Babu kasar da ta kai Najeriya cigaba a nahiyar Afrika - Buhari

- Najeriya za tayi murnan cika shekaru 60 da samun yanci ranar 1 ga Oktoba 2020

- An sanya murnan bana take "Shekaru 60 tare"

- Buhari ya ce ba za'ayi shagalin da ya kamata ba amma shekara guda za'ayi ana murnar wannan rana

Shugaba Muhammadu Buhari ya alanta cewa Najeriya ce kasar bakaken fata mafi cigaba a fadin duniya, amma cutar COVID-19 za ta hanasu yin shagalin da ya kamata domin murnar cika shekaru 60 da samun yancin kai.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne a bikin kaddamar da take da tambarin shirin murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun yanci daga wajen turawan mulkin mallaka.

Hakan ya biyo bayan maganar gwamnati cewa shekara daya za'a kwashe ana murnar cika shekaru 60 daga yanzu zuwa ranar 30 ga Satumba, 2021.

Taron ya gudana ne a taron majalisar zartaswar a fadar shugaban kasa, Aso Villa.

KU KARANTA: Ana shirin shigo da kaji masu dauke da cutar Korona Najeriya - Hameed Ali, CG Kwastam

Buhari yace: "Kalan koren da ke jikin tutarmu na tunatar da mu soyayya, yalwataccen arziki da yawan al'umma da aka azurtamu da shi"

"Dukkan wadannan ne suka zamar da kasar bakaken fata mafi cigaba a duniya kuma kasa mafi girman tattalin arziki a nahiyar Afrika."

"Iyayenmu, duk da banbancin addini, kabila da harshe, sun hada kai wajen kwato wa Najeriya yanci."

Nigeria@60: Babu kasar da ta kai Najeriya cigaba a nahiyar Afrika - Buhari
Nigeria@60: Babu kasar da ta kai Najeriya cigaba a nahiyar Afrika - Buhari
Source: Twitter

DUBA NAN: Yan Boko Haram na cin karnukansu ba babbaka a Arewa maso gabas da yamma kulli yaumin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya kaddamar da sabon logon kasar, wanda za a yi amfani da shi wurin shagalin bikin murnar zagayowar ranar samun 'yancin.

An kaddamar da sabon tambarin ne yayin taron majalisar zartarwa na tarayya da aka yi a Abuja, babban birnin kasar.

Ministocin tarayya da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne suka samu halarta, Channels TV ta wallafa.

Ministocin sun hada da ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, da sauransu.

A tun farko watan Satumban shekarar nan ne gwamnatin tarayya ta bukaci masu hazakar kirkire-kirkire da zane, da su kawo zane wanda za a yi amfani da shi a yayin da kasar ke cika shekaru 60 da samun 'yancin kai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel