An tirsasa wani mutum ya auri gawar budurwarsa da ya dirka wa ciki ta mutu yayin haihuwa

An tirsasa wani mutum ya auri gawar budurwarsa da ya dirka wa ciki ta mutu yayin haihuwa

- Wani matashin dan kassar Mozambique ya shiga mawuyacin hali bayan da aka tirsasa shi auren gawar budurwarsa

- Tun farko dai masoyan biyu suna zama tare amma basu yi aure ba har budurwar ta samu ciki sannan ta mutu wurin haihuwa

- Hakan yasa 'yan uwanta suka ce ba za su birneta ba har sai saurayin nata ya biya sadaki an daura musu aure kamar yadda yayi alkawari kafin mutuwarta

Wani matashi mazaunin yankin kudancin Inhamben an tirsashi biyan sadakin budurwarsa, wanda ake kira da "Lobolo" wacce ta mutu a cikin kwanakin karshen mako, gidan rediyon Mozambique ya ruwaito.

Bayan ta rasu sakamakon matsalar da ta samu wurin haihuwa, 'yan uwanta sun tirsasa saurayinta da ya biya sadakinta, sun ja kunnen cewa ba zasu birneta ba.

'Yan uwan budurwar sun zargi matashin da kin cike alkawarinsa wanda ya hada da kai gaisuwa gidansu budurwar kafin aukuwar mummunan lamarin.

Domin tabbatar da an yi bikin birneta, matashin ya ce sai ya siya sabbin kaya da takalma domin gawar, kuma ya amince zai biya dala 800 tare da yin bikin aurensu a ranar 15 ga watan Disamba.

Wani dan uwan matashin, Irmao do Jovem, ya yi bayanin lamarin dalla-dalla.

"Mun yi kokarin tattara kudin da suka bukata, amma mun kasa. Mun hada dala 178. Don haka dole ta sa muka sa hannu a kan wata yarjejeniya da tace za mu biya ragowar kudin kafin ranar auren," yace.

A yayin da 'yan uwan matashin suke kokarin bada duk abinda aka bukata, sun kushe halayyar 'yan uwan marigayiyar, Vanguard ta wallafa.

Amma kuma, wannan lamarin ya saba faruwa a sauran kabilun da ke Mozambique, ballantana idan namiji ya yanke shawarar zama da mace ba tare da sun yi aure ba.

KU KARANTA: Boko Haram: Dahiru Bauchi, ya musanta goyon bayan Mailafia a kan ikirarinsa

An tirsasa wani mutum ya auri gawar budurwarsa da ya dirka wa ciki ta mutu yayin haihuwa
An tirsasa wani mutum ya auri gawar budurwarsa da ya dirka wa ciki ta mutu yayin haihuwa. Hoto daga Vanguard
Source: Getty Images

KU KARANTA: Motocin kudin da ka kwamushe a gidanka ba za su iya siya maka Edo ba - Ikimi ga Tinubu

A wani labari na daban, wani babban fasto mai shekaru 57, mai suna Ebenezer Ogunmefun, ya shiga hannun 'yan sanda kuma an gurfanar da shi a gaban wata kotun majistare da ke zama a Abeokuta.

Ana zargin babban faston da yi wa yarinya mai shekaru 15 fyade, wacce mahaifiyarta ta kai ta cocin don tsarkakewa.

A yayin da aka gurfanar da faston a kan zargin cin zarafi, dan sanda mai gabatar da kara, sifeta Moshood Hammed, ya sanar da kotun cewa faston yana zama ne garin Abeokuta.

Faston na zama a gida mai lamba daya, titin Farfesa Ajibo Toluca a yankin Olomore da ke Abeokuta a jihar.

Ya sanar da cewa mahaifiyar yarinyar da kanta ta mika ta ga faston domin 'tsarkakewa' daga miyagun aljanu.

Faston ya sa yarinyar ta yi rantsuwa da bibul cewa ba zata sanar da kowa cewa ya yi mata fyade ba yayin da yake raba ta da miyagun aljannun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel