An bawa wata budurwa marainiya da bata da hannu kyautar wani kyakkyawan gida mai dakuna uku

An bawa wata budurwa marainiya da bata da hannu kyautar wani kyakkyawan gida mai dakuna uku

- Wata budurwa mai suna Ana Aniwetalu, anyi mata goma ta arziki, yayin da cocin da take zuwa ta bata kyautar gida mai dakuna uku

- Shugaban cocin, Valerian Okeke, wanda ya taimakawa budurwar yace bai son kowa ya san abin arzikin da yayi

- Budurwar wacce bata da hannu tayi kukan murna sosai

Wata marainiya da bata da hannu mai shekaru 21, da ake kira da suna Ada Aniwetalu, anyi mata goma ta arziki, yayin da aka bata kyautar sabon gida mai dan karen kyau da yake dauke da dakuna har guda uku a ciki, sannan kuma aka dauki nauyin karatun ta.

Ada dai an haifeta ba tare da hannu ba, amma hakan bai hanata amfani da kafarta wajen gabatar da harkokinta na rayuwa ba.

Ba wai iya tafiya kawai take yi da kafarta ba, tana amfani da kafarta tana rubutu da kuma sauran abubuwa na cikin gida.

An bawa wata budurwa marainiya da bata da hannu kyautar wani kyakkyawan gida mai dakuna uku
Marainiya da bata da hannu da aka yiwa goma ta arziki
Source: Original

Budurwar mai shekaru 21 da aka haifeta a jihar Anambra a garin Nteje dake cikin karamar hukumar Oyi, Ada marainiya ce, wannan nakasa da take da shi bai hanata cimma burinta na rayuwa ba.

Wannan kokari da budurwar take da shi ya sanya wata coci karkashin jagorancin shugabanta Archbishop Valerian Okeke, suka taimaka mata da wannan abin arziki.

KU KARANTA: Matar da tace takalmi yafi kanin mijinta daraja tayi dana sani bayan yayi kudi yayi mata goma ta arziki

Bayan jin labarinta, wannan fasto ya bata kyautar gida mai dan karen kyau da kuma daukar nauyin karatunta baki daya.

A wata hira da yayi da wakilin Legit.ng a jihar Imo, Victor Duru, wanda yake na hannun daman shugaban cocin, wanda yayi magana a madadinsa ya bayyana abinda ya sanya suka taimaki wannan yarinya.

Ya ce: "Archbishop yayi mamaki sosai da har wannan abu da yayi ya yadu a shafukan sadarwa, saboda baya so kowa ya sani, yana son yayi komai cikin sirri, hakan ya sanya bai ji dadi ba ko kadan da labarin ya fita.

"Bamu kira kowa ba a lokacin da muka bata kyautar gidan, akwai yiwuwar mutanen da suka halarci wajen ne suka dauki hoto da wayoyinsu suka sanya a shafukan sadarwa.

KU KARANTA: Babu dadewa za mu samu man fetur a farashi mai sauki - FG

"Archbishop din ya ce wannan sadaka ce yayi, akan abinda ya yarda da shi. Ba a yin sadaka kuma a dinga yadawa. Idan ban manta ba, littafin Injila ya ce: 'Kada ka bari hannunka na hagu ya san abinda ka bayar da hannunka na dama'.

"Wannan shine halayen Archbishop, saboda haka ya sanya bai bayyanawa duniya ba."

A yanzu dai wannan budurwa tana da gida nata na kanta sannan kuma za ta iya fita neman ilimi kamar yadda take so.

Ita kuwa wata mata daga jihar Enugu mai suna Josephine Nchetaka Chukujama Eze, ta nuna ainahin adalci bayan ta mayar da kimanin naira miliyan goma sha hudu da aka yi kuskuren aikawa zuwa asusunta na banki.

Mijinta wanda yake dan jarida ne kuma lauya, Chukujama Eze, ya bayyana haka ga News Express yayin da yake yabon matarshin akan abin kirkin da tayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel