Da duminsa: Mun sallami masu cutar Korona kimanin 3500 a yau kadai - NCDC

Da duminsa: Mun sallami masu cutar Korona kimanin 3500 a yau kadai - NCDC

- Da alamun Najeriya na samun nasara wajen yaki da cutar Coronavirus

- A cikin kwanakin baya-bayan, adadin masu waraka ya ninka na sabbin masu kamuwa

- An fara kulle cibiyoyin jinyar masu cutar saboda babu sauran marasa lafiya

Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa an sallami mutane 3442 dake fama da cutar Korona a birnin tarayya Abuja, jihar Kwara da wasu jihohin Najeriya a yau kadai.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:30 na daren ranar Laraba 16 ga Satumba, shekarar 2020.

Hukumar ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 126 a fadin Najeriya.

Jawabin hukumar yace: "Warakan da muka samu yau mutane 2,967 a birnin tarayya da 103 a jihar Kwara da aka yiwa jinya cikin gida bisa sharrudan da hukumar ta gindaya."

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 126 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

FCT-37, Lagos-27, Plateau-16, Kaduna-9, Abia-7, Gombe-6, Ondo-6, Imo-5, Delta-2, Ekiti-2, Kwara-2, Oyo-2, Bauchi-1, Kano-1, Katsina-1, Ogun-1, Yobe-1.

Kawo yanzu, jimillan mutane 56,604 suka kamu da cutar a Najeriya, yayinda 47,872 suka warke, 1,091 sun mutu.

KU DUBA NAN: Ana shirin shigo da kaji masu dauke da cutar Korona Najeriya - Hameed Ali, CG Kwastam

Da duminsa: Mun sallami masu cutar Korona kimanin da 3500 a yau kadai - NCDC
Da duminsa: Mun sallami masu cutar Korona kimanin da 3500 a yau kadai - NCDC
Asali: Twitter

DUBA NAN: Yan APC a Edo na karban katin zaben mata suna basu Atamfa (Bidiyo)

A bangare guda, Ministan kula da harkokin yankin Neja Delta, Godwill Akpabio, ya musanta zargar 'yan majalisar tarayya da yayi da samu daga kwangilar hukumar kula da harkokin Neja Delta (NDDC).

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Akpabio yayin jawabi ga kwamitin majalisar wakilai a yayin binciken batan dabon da N40 biliyan tayi daga hukumar, ya yi barazanar wallafa jerin sunayen wasu 'yan majalisa da suka amfana da kwangilar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel