Yan APC a Edo na karban katin zaben mata suna basu Atamfa (Bidiyo)

Yan APC a Edo na karban katin zaben mata suna basu Atamfa (Bidiyo)

- Tun kan ranar zabe, an fara amsan katunan zaben mutane don wasu dalilai

- Yayinda wasu ke karban katunan don yin magudi, wasu na yi don hana wasu zababbun mutane zabe

- Gwamnatin Amurka da Birtaniya sun lashi takobin hukunta duk wanda yayi magudi a zaben Edo

Ana saura kwanaki 3 zabe, wani faifan bidiyo ya bayyana a kafafen ra'ayi da sada zumunta wanda ke nuna masu yakin neman zabe suna amsan katin zaben mata suna basu turmin Atamfa.

Dubi ga irin hulunan da masu raba atamfofin suke sanye da su, ya nuna cewa suna 'POI' wanda ke nufin dan takaran jam'iyyar All Progressives Congress APC.

Hakazalika daya daga cikin yan matan ta sanya dankwalin jam'iyyar APC.

Za'a gudanar da zaben jihar Edo ne ranar 19 ga Satumba, 2020.

Za a goge raini ne tsakanin gwamnan jihar, Godwin Obaseki, kuma dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, da Fasto Osaze Ize-Iyamu na jam'iyyar All Progressives Congress APC.

KU KARANTA NAN: Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i ya rattada hannu kan dokar Penal Code 2020, wacce ta tanadi dokar dandaka ga duk wanda aka kama da laifin fyade a jihar.

Kalli bidiyon da jaridar Cable ta samu:

A ranar Litinin, Gwamnatin Amurka ta ce ta saka wa wasu mutane takunkumi hana su shigar ƙasar ta saboda magudin zabe da suka yi yayin zabukkan gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa da aka yi a 2019.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake shirin yin zabukkan gwamnoni a jihohin Edo da Ondo a watan Satumba da Oktoba na 2020.

Duk da cewa ba a riga an yi zabuka a Edo da Ondo ba, Sakataren Gwamnatin Amurka Mike Pompeo ya ce akwai wasu da aka haramta musu shiga kasar ta Amurka.

Hakan na cikin wata sanarwa ne mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun ma'aikatar wajen Amurka, Morgan Ortagus da ya fitar a ranar Litinin.

DUBA NAN: Ana shirin shigo da kaji masu dauke da cutar Korona Najeriya - Hameed Ali, CG Kwastam

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel