Babu dadewa za mu samu man fetur a farashi mai sauki - FG

Babu dadewa za mu samu man fetur a farashi mai sauki - FG

- Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa nan babu dadewa za a fara samun man fetur a farashi mai sauki

- Ministan yada labarai da al'adu na Najeriya, Lai Mohammed ya sanar da hakan a jihar Imo da ke kudancin Najeriya

- Ya ce kafaf kananan matatun man fetur a fadin kasar nan zai shawo kan matsalar damuwar da aka shiga a kan cire tallafin man fetur

Gwamnatin tarayya ta tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa nan ba da dadewa ba za a siyar da man fetur a farashi mai matukar sauki, Vanguard ta wallafa.

Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana hakan a karamar hukumar Egbema da ke jihar Imo yayin rangadin da ya je karamar matatar man fetur da za a kaddamar a wata mai zuwa.

Da irin wannan matatun, ministan ya ce dukkan magana a kan tallafin man fetur zai zama maras amfani saboda za a dinga samunsa a farashi kalilan.

Ya bayyana kafa kananan man fetur din a kasar na da wata hanya da za a samu sauki a wannan mulkin na shugaba Buhari.

"Za mu iya bayyanawa 'yan Najeriya cewa, kusan kowacce gwamnati a Najerya ta dinga magana a kan kananan matatun man fetur. Babu gwamnatin da za ta ki aminta da wannan lamari," yace.

KU KARANTA: Za a fara rataye masu yiwa mata fyade ko kuma a basu guba a kasar Pakistan

Babu dadewa za mu samu man fetur a farashi mai sauki - FG
Babu dadewa za mu samu man fetur a farashi mai sauki - FG. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Najeriya ce kasar da tafi kowacce kasar bakar fata cigaba a duniya - Shugaba Buhari

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, ya ce gwamnatin tarayya ta hana shigo da kayan abinci ne domin ta bunkasa aikin noma tare da tseratar da 'yan Najeriya daga rashin aikin yi.

Ya jaddada cewa, noma babbar hanya ce ta samar da ababen bukata, rage zaman kashe wando da fatattakar talauci daga kasar nan, Channels TV ta wallafa.

"Domin ganin mun dawo da samar da kayan bukata, dole ne marasa aikin yi ballantana wadanda basu yi karatu ba su fada harkar noma.

"Da ace bamu koma gona ba, da yanzu muna cikin matsala. Hakan ne yasa dole aka haramta shigo da kayayyakin abinci domin samar da aiki," shugaban kasa yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel