Gwamnatin Katsina za ta bawa tubabbun 'yan bindiga gidaje da shaguna da gonaki

Gwamnatin Katsina za ta bawa tubabbun 'yan bindiga gidaje da shaguna da gonaki

- Gwamnatin jihar Katsina ta bullo da sabon tsarin janyo hankalin 'yan bindiga a jihar su ajiye makamansu su rungumi zaman lafiya

- Gwamnatin jihar tana shirin gina rukunin gidaje da shaguna a kusa da wasu dazuka a jihar inda za a bawa tubabbun 'yan bindigan su zauna

- Gwamnatin jihar na sa ran gine rukunin gidaje a kusa da dazukan sai kori duk wasu 'yan bindiga da ke buya a cikin dajin ya kuma bawa tubabbun yan bindigan damar fara sabon rayuwa

Gwamnatin jihar Katsina ta bullo da sabbon tsari don kawo karshen hare-haren 'yan bindiga a jihar kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Gwamnatin ta yi alkawarin bada gidaje, shaguna da filayen noma ga 'yan bindigan da suka amince za su ajiye makamansu su mika kai ga jami'an tsaro.

DUBA WANNAN: Adamawa: Tsohon gwamnan PDP, Ngillari ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Gwamnatin Katsina za ta bawa 'yan bindiga gidaje da shaguna a kasuwanni
Gwamnatin Katsina za ta bawa 'yan bindiga gidaje da shaguna a kasuwanni
Asali: Twitter

Wani daga cikin shugabannin 'yan bindiga mai suna Sada ya mika wuya ga sojojin na musamman na Fowarda Base da ke Dansadau.

Ya mika bindigu AK 47 guda uku da sub-machine gun da alburusai.

Sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa ne ya sanar da shirin sassaucin da Gwamna Aminu Masari zai yi wa 'yan bindigan da suka tuba yayin taron manema labarai a gidan gwamnati.

KU KARANTA: Bidiyo: Sojoji sun tarwatsa mafakan shugabannin 'yan bindiga Damina da Sani Mochoko a dajin Kuyambana a Zamfara

Inuwa, ya kuma ce gwamnatin jihar kawo yanzu ta tallafawa hukumomin tsaro da Naira biliyan 4.274.

Ya ce gwamnatin jihar za ta gina gidajen ne a kusa da dajin Rugu, Yantumaki, Maidabino da Sabwa/Faskari.

A cewarsa, za a tanadi makarantu, cibiyoyin lafiya kasuwanni da filayen noma a rukunin gidajen da za a gina wa tubabbun 'yan bindigan.

"Mun kammala shiri ga wadanda suka amince za su zauna a kusa da dajin Rugu, wannan na cikin tsarin da gwamnati ke yi na hana 'yan bindiga zama a cikin dajin, kwamitin da aka kafa za ta fara aiki kowanne lokaci daga yanzu.

"Wasu wuraren da ake ganin yiwuwar gina rukunin gidajen sun hada da dajin Yantumaki, Maidabino, Sabwa da Faskari."

Inuwa ya kuma ce tunda Shugaban kasa ya bada umurnin a canja tsarin yaki da 'yan bindigan an fara samun saukin hare hare a jihar.

A wani labarin daban, kun ji cewa wasu ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun kashe wani Alhaji Mai Yadi sun kuma sace ɗansa, Usman a garin Ƴankara da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayin, Kwamared Younusa Mukhtar ya tabbatar da afkuwar hakan a ranar Talata 15 ga watan Satumba ya ce lamarin ya faru misalin ƙarfe 11 na daren ranar Litinin a gidansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel