Duk da bakar wahalar dana sha a kasar Libya, har yanzu ina son komawa can

Duk da bakar wahalar dana sha a kasar Libya, har yanzu ina son komawa can

- Wata budurwa mai suna Irene Ehime, da ta dawo daga kasar Libya ta ce tana so ta koma kasar saboda abubuwa babu sauki a Najeriya

- Budurwar ta bayyana yadda rayuwarta ta kasance a kasar ta Libya, yadda aka yi mata fyade aka azabtar da ita

- Ehime ta ce inda ace tana da wanda zai taimaka mata da 'ya'yanta ko tunanin zuwa kasar Libya baza tayi ba

Wata mata 'yar Najeriya mai suna Irene Ehime ta bayyana labarin rayuwar da tayi mai ban wahala a lokacin da take kasar Libya.

A wata hira da tayi da Legit TV, matar mai shekaru 25 ta ce ta je kasar Libya ne da niyyar shiga kasar Spain.

Matar wacce take da yara guda biyu, wacce mijin yaran ya mutu, ta ce an sha yi mata fyade da azabtar a kasar ta Libya.

Ta ce mutanen da suka kai ta kasar ta Libya basu sanar da ita cewa za ayi mata wannan cin mutuncin ba, ta kara da cewa bata ji dadi ba ko kadan bayan wannan abu da ya faru da ita.

Duk da bakar wahalar dana sha a kasar Libya, har yanzu ina son komawa can
Duk da bakar wahalar dana sha a kasar Libya, har yanzu ina son komawa can
Source: UGC

Sai dai kuma, Irene ta bayyana cewa tana so ta koma kasar ta Libya, saboda abubuwa sun yi mata wuya a Najeriya.

Ta ce: "Ina shan bakar wahala matuka, saboda ina so na dauki nauyin yarana na basu karatu mai kyau."

Bayan labarin Irene, akwai wata budurwa mai shekaru 24 da aka bayyana sunanta da Omolara Akintayo ta ce tayi dana sanin zuwa kasar Libya neman arziki.

KU KARANTA: Idan har Buhari bai canja takunsa ba nan da 2023 Najeriya za ta zama ba tamu ba - Fani Kayode

A wata hira da tayi da Legit TV, matashiyar budurwar ta ce ta tafi kasar ta Libya ne saboda iyayenta na cikin matsanancin hali na talauci.

Omolara ta bayyana irin halin da ta shiga akan hanyarta ta zuwa kasar ta Libya, inda ta ce ta shafe kwanaki 14 akan hanya kafin su karasa kasar.

KU KARANTA: Za a fara rataye masu yiwa mata fyade ko kuma a basu guba a kasar Pakistan

A cewarta, a lokacin da suke tsakiyar sahara, da yawa daga cikin mutane sun mutu, wasu kuma an sanya su dole suka sha ruwan kashi, saboda babu ruwa mai kyau ko abinci.

Omolara ta ce biyu daga cikin kawayenta anyi musu fyade a tsakiyar sahara akan hanyarsu ta zuwa Libya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel