Wawure kudin kwangilar NDDC: Akpabio ya yi sabuwar magana a kan 'yan majalisa

Wawure kudin kwangilar NDDC: Akpabio ya yi sabuwar magana a kan 'yan majalisa

- Ministan kula da harkokin Neja Delta, Sanata Godwill Akpabio ya janye kalamansa na cewa 'yan majalisar tarayya ne suka karbe kwangilar NDDC

- Tsohon gwamnan kuma minista a halin yanzu, ya ce kakakin majalisar wakilai bai taba ce masa ya wallafa sunayen wadanda suka mora daga kwangilolin ba

- Ya yi wannan jawabin ne bayan ganawar sirri da yayi da sabon magatakardan majalisar dattawa

Ministan kula da harkokin yankin Neja Delta, Godwill Akpabio, ya musanta zargar 'yan majalisar tarayya da yayi da samu daga kwangilar hukumar kula da harkokin Neja Delta (NDDC).

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Akpabio yayin jawabi ga kwamitin majalisar wakilai a yayin binciken batan dabon da N40 biliyan tayi daga hukumar, ya yi barazanar wallafa jerin sunayen wasu 'yan majalisa da suka amfana da kwangilar.

Ministan ya ce, "Su waye suka fi mora daga kwangilolin? Ku ne daga majalisar dattawa."

Amma yayin jawabi ga manema labarai a ranar Talata bayan taron sirri da yayi da magatakardan majalisar dattawa, Amos Olatunde-Ojo, minsitan ya soke wannan zargin inda yace rashin fahimta ne.

A kan tambayar da aka yi masa na ko ya cike sharadin da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila yayi masa, na cewa ya wallafa sunaye, Akpabio ya ce: "A'a, ka yi kuskure. Ba haka mai girma kakakin yace ba."

"Kakakin majalisar ya so sani ko akwai wani nau'i na tirsasawa ne yayin da 'yan majalisar suka karba kwangilar daga NDDC. Bai bukaci sunayen 'yan kwangilar ba, yanzu na fara ji daga bakin ku."

A kan dalilinsa na ziyarar, ya ce: "Na zo ne domin in taya shi murnar cigaba da ya samu kuma in nemi goyon bayan majalisar dattawan wurin cigaban yankin Neja Delta.

"A kowanne fanni, ni sanata ne. Ganina a majalisar dattawa bai kamata ya zama abun mamaki ba. Babu wanda yake kirana da Gwamna Akpabio, amma koyaushe sanata Akpabio ake kirana. Gida na zo."

KU KARANTA: Cikar Najeriya shekaru 60: Buhari ya kaddamar da sabon tambari (Hotuna da Bidiyo)

Wawure kudin kwangilar NDDC: Akpabio ya yi sabuwar magana a kan 'yan majalisa
Wawure kudin kwangilar NDDC: Akpabio ya yi sabuwar magana a kan 'yan majalisa. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: Katsina: 'Yan bindiga sun kashe Sarkin Tauri da wani mutum 1, sun sace mutane masu yawa

A wani labari na daban, majalisar wakilan Najeriya ta bada umarnin damko mukaddashin manajan daraktan kwamitin rikon kwarya na hukumar habaka yankin Neja Delta, Farfesa Kemebradikumo Pondei a kan yadda ya fice daga majalisar babu izini.

Idan za mu tuna, ana bincikar pondei ne a kan wasu miliyan N40 da suka yi batan dabo a hukumar, ya fice daga majalisar a ranar Alhamis yayin da ake bukatar jin ta bakinsa.

Shugaban NDDC ya zargi shugaban kwamitin majalisar wakilan masu alhakin bincikarsu, Olubunmi Tunji-Ojo, da rashawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel