Sokoto: Mutane 80,405 za su samu tallafi daga gwamnatin tarayya - NEMA

Sokoto: Mutane 80,405 za su samu tallafi daga gwamnatin tarayya - NEMA

- A kalla mutane 80,405 ne za su amfana da tallafin hatsi a jihar Sokoto da gwamnatin tarayya ta bayar ta hannun hukumar NEMA

- Shugaban NEMA na kasa, Muhammadu Muhammed ne ya sanar da hakan yayin da ya ke gabatar da hatsin ga gwamnatin Sokoto inda ya ce an bayar don tallafawa marasa karfi su rage radadin kullen korona

- Gwamnatin jihar Sokoto ta jinjinawa gwamnatin tarayya game da bayar da tallafin ta kuma yi alkawarin za a raba wa wadanda ya dace a kan lokaci

Hukumar bayar da agajin gaggawa na kasa, NEMA, ta fara rabon hatsi tan 3,659.7 ga gidaje 80,405 a jihar Sokoto a wani mataki na tallafa musu sakamakon matsin da suka shiga yayin kullen annobar korona.

Shugaban NEMA na kasa, Muhammadu Muhammed ne ya bayyana hakan yayin da ya ke mika wa gwamnatin jihar Sokoto kayan abincin a gidan gwamnati a ranar Talata a Sokoto.

DUBA WANNAN: Kuma dai: An sake sace jami'in DSS, an nemi N100m a matsayin kudin fansa (Hotuna)

Sokoto: Mutane 80,405 za su samu tallafi daga gwamnatin tarayya - NEMA
Sokoto: Mutane 80,405 za su samu tallafi daga gwamnatin tarayya - NEMA. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

Mista Muhammed wanda ya samu wakilcin Dr Onimode Bandele, ya ce gwamnatin tarayya ta samar da hatsi da za a raba wa mutane masu karamin karfi a jihar domin rage radadin kullen korona da aka saka don dakile yaduwar annobar.

Ya ce: "Muna mika hatsi daban-daban daga rumbun gwamnatin tarayya da Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a bayar.

"An bayar da hatsin ne domin a raba a matsayin tallafi ga marasa karfi da kullen cutar korona ta shafa."

KU KARANTA: A wurin caca miji na ya ke kashe dukkan kudinsa: Mata ta nemi kotu ta datse igiyar aurenta

Mista Muhammed ya ce hatsin da aka bayar sun hada da tan 1.701.6 na masara, tan 173.10 na gero da tan 1.785 na dawa.

Shugaban na NEMA ya janyo hankalin gwamnatin jihar a kan hasashen ruwan sama da ambaliya da aka yi na shekarar 2020.

Muhammad ya ce akwai bukatar gwamnatin jihohi su dauki matakan kiyaye afkuwar ambaliyar musamman a yanzu da damina ta yi nisa.

A jawabinsa, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya jinjinawa gwamnati bisa tallafin inda ya ce zai taimaka sosai wurin rage wa mutane wahalhalun da suke ciki.

Mista Tambuwal wanda Saidu Umar, Sakataren Gwamnatin Jihar ya wakilta ya ce, hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar, SEMA, za ta tabbatar an raba wa mutane kayan tallafin a lokacin da ya ce.

A wani labarin kun ji cewa Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane na Ƙasa, NAPTIP ta ce ta ceto mutane 135 tare da kama mutum 86 da ake zargin masu safarar mutane ne a Kano daga watan Janairu zuwa yanzu.

Kwamandan hukumar a jihar Kano, Shehu Umar ne ya bayyana hakan yayin hirar da Kamfanin dillancin labarai, NAN, ta yi da shi ranar Talata a Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel