Idan har Buhari bai canja takunsa ba nan da 2023 Najeriya za ta zama ba tamu ba - Fani Kayode
- Tsohon ministan Najeriya ya ce matukar Buhari ya cigaba da irin wannan mulkin to tabbas nan da 2023 babu abinda zai rage a Najeriya
- Tsohon ministan ya ce yanzu kowa a Najeriya ya gaji da mulkin shugaban kasar inda kungiyoyi daga yankin Kudu da Arewa ke fitowa suna bukatar a ware musu bangarensu
- Ya ce ko dai shugaban kasar ya canaja ko kuma kasar ta lalace nan ba da dadewa ba
Tsohon ministan jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya ce har sai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya canja takunsa akan tafiyar da lamarun Najeriya, sannan komai zai dawo daidai, idan ba haka ba kuma nan da 2023 za a nemi Najeriya a rasa.
Femi Fani Kayode ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya da daddare.
Wannan rubutu na shi dai ya zo ne kwanaki kadan bayan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa Najeriya na cigaba da lalacewa a hankali a hankali a karkashin gwamnatin shugaba Buhari.
Fani Kayode ya ce:
"A shekarar 2015 na ce Buhari zai raba kan Najeriya, baku yadda dani ba.
"A shekarar 2017, na ce Buhari ya raba Najeriya, kuka ki yadda da magana ta.
"A shekarar 2019 na ce Buhari ya tura Najeriya hanya marar bullewa, baku yadda da magana ta ba.
"A yau na ce idan har Buhari bai canja takunsa ba kuma mun gina katanga a tsakaninmu ba, nan da 2023 babu abinda zai rage a Najeriya.
KU KARANTA: Ka kyale Obaseki, ka fuskanci makiyan siyasa na APC - PDP ga Tinubu
"A yanzu haka sama da shekaru biyar da suka wuce maganganu na sun zama gaskiya.
"Wadanda suke tantamar abinda na fada su cigaba da yi, saboda na san hakan babu abinda zai rage a jikina. Sakon da yake cikin magana ta shine mafi muhimmanci ba abinda kuke tunani a kai na ba.
"Babban abin bacin ran shine wanda ya zama jigo wajen rabuwar kan Najeriya, kuma wanda kullum mutane ke tunanin shine yake daidai shine Buhari.
"Yayi musu aiki sosai, saboda ba wai iya raba kan Najeriya yayi ba, ya yanka kasar ne ya raba ta gida-gida, sannan ya binneta a wurare daban-daban.
"Kasar mu abar alfaharin mu an mika mishi ita a shekarar 2015 amma ya fasa ta, ya cire mata numfashi.
"A yau za ku ga dubunnan mutane a yankin kudu maso yamma suna yawo akan tituna suna bukatar a ware musu bangarensu a Najeriya.
KU KARANTA: UK tana barazanar kwace kadarorin 'yan siyasar da za su yi magudi a zabukan Edo da Ondo
"Haka a bangaren kudu maso gabas, suma sun fito suna so a raba kasar a basu kason su."
"Hatta mutanen arewa sun fito cikin bacin rai sun nuna cewa abinda ake yi musu ya ishe su."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng