'Yan Najeriya na kira ga wata 'yar Kano da ke aikin soja a Amurka da ta dawo Najeriya don taimakon kasarta

'Yan Najeriya na kira ga wata 'yar Kano da ke aikin soja a Amurka da ta dawo Najeriya don taimakon kasarta

- Ayshatu Jibo soja ce 'yar Najeriya da ke aiki da rundunar sojin kasar Amurka, 'yar asalin jihar Kano ce

- Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani na Twitter ya yi kira ga jarumar da ta dawo domin bautawa kasarta ta gado

- Ayshatu tana daya daga cikin 'yan Najeriya da suke fidda kasar kunya a fannoni daban-daban a kasashen ketare

Wani dan Najeriya a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ya yi kira ga wata 'yar Najeriya daga jihar Kano da ke aiki da rundunar sojin Amurka da ta dawo gida.

Kamar yadda wallafarsa ta bayyana, ya bukaci Ayshatu Jibo da ta dawo gida domin bai wa kasarta ta gado kariya a maimakon bautawa kasar Amurka.

Wannan wallafar ta janyo cece-kuce daga jama'a masu tsokaci. Wasu sun goyi bayan wallafar yayin da wasu suka dinga caccakar mai wallafar tare da zargarsa da nuna halayyar mugunta.

Ga dai yadda aka dinga tsokaci:

KU KARANTA: Budurwa ta rayu bayan ta fado daga bene mai hawa 8, yayin da take gujewa saurayinta

KU KARANTA: Bidiyon wajen da aka binne marigayi Sanata Ajimobi da aka cika wajen da kayan alatu, da wutar lantarki wacce bata daukewa

Akwai 'yan Najeriya masu tarin yawa da ke cikin rundunar sojin Amurka kuma suka zama ababen alfahari.

Daya daga cikinsu ita ce Ruth Inomina, wacce ba a dade da rantsar da ita ba a cikin rundunar sojin ruwa na Amurka.

A wani labari na daban, Ayo Balogun, shahararren mawaƙin Najeriya wanda aka fi sani da Wizkid, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari da takwaran sa na Amurka, Donald Trump, ko kadan ba su da damu da al'ummar su ba.

Cikin wani sako da ya wallafa a kan shafin sa na Twitter, gogarman mawakin ya ce banbancin da ke tsakanin shugabanin biyu shi ne kwazon Trump na iya amfani da dandalin sadarwa na Twitter.

Wizkid ya ce Buhari ya jahilci iya amfani da dandalin na sadarwa, lamarin da ya ce shi ne kadai banbancin da ke tsakanin shugabannin biyu.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, Wizkid wanda bai taɓa yin sharhi ko furuci a kan kowane dan siyasa ba, a yau ya ba 'yan Najeriya mamaki da sauran al'ummar duniya.

Mawakin ya yi furuci a kan shugabannin biyu, biyo bayan yadda jami'an tsaro na 'yan sanda ke kashe mutane ba tare da wani dalili ba a kasar Amurka da kuma nan gida Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel