Kuma dai: An sake sace jami'in DSS, an nemi N100m a matsayin kudin fansa (Hotuna)

Kuma dai: An sake sace jami'in DSS, an nemi N100m a matsayin kudin fansa (Hotuna)

- Awanni kadan bayan wasu 'yan bindiga sun kashe jami'in DSS, Sadiq Bindawa a Katsina, an sake garkuwa da wani jami'in a Kaduna

- Rahotanni sun ce 'yan bindigan sun sace jami'in ne tare da dansa mai shekaru hudu a hanyar Rigachikun zuwa Afaka a Kaduna

- Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan jami'in da ba a bayyana sunansa ba sun nemi a biya N100m kudin fansarsa

'Yan bindiga sun sace jami'in hukumar 'yan sandan farin kaya, DSS, tare da dansa mai shekaru hudu a ranar Asabar a jihar Kaduna.

Jami'in da a yanzu ba a bayyana sunansa ba ya fada hannun masu garkuwar ne a hanyar Rigachikun zuwa Afaka a ranar Litinin kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Kuma dai: An sake sace jami'in DSS, an nemi N100m a matsayin kudin fansa
Kuma dai: An sake sace jami'in DSS, an nemi N100m a matsayin kudin fansa. Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

Kuma dai: An sake sace jami'in DSS, an nemi N100m a matsayin kudin fansa
Kuma dai: An sake sace jami'in DSS, an nemi N100m a matsayin kudin fansa. Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

KU KARANTA: Adamawa: Tsohon gwamnan PDP, Ngillari ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Kuma dai: An sake sace jami'in DSS, an nemi N100m a matsayin kudin fansa
Kuma dai: An sake sace jami'in DSS, an nemi N100m a matsayin kudin fansa. Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

Rahotanni sun ce yan bindigan sun tuntubi iyalansa sun nemi a biya su kudin fansa Naira miliyan 100 kafin su sako shi.

DUBA WANNAN: Bidiyo: An tilasta wa ɓarawon kaza cin ɗanyen kazar da aka kama shi ya sata

Jami'in da aka yi garkuwa da shi yana aiki ne a matsayin mai kula da inda ake ajiye makamai na makarantar horas da sabbin jami'an DSS.

Hakan na zuwa ne awanni kadan bayan yan bindiga sun kashe wani jami'in DSS mai shekaru 33 mai suna Sadiq Abdullahi Bindawa duk da kudin fansa Naira miliyan 5 da aka biya.

Marigayi Bindawa yana gidansa ne da ke bayan sakatariyar gwamnatin tarayya a Katsina yayin da yan bindigan suka kai masa hari. Bindawa yana aiki ne da sashin tattara bayannan sirri na hukumar da ke Abuja.

Kamar yadda lamarin ya ke a wasu sassan kasar nan, ana samun hare haren 'yan bindiga da garkuwa da mutane a jihohin Kaduna da Katsina a cikin makonnin da suka gabata.

A wani rahoton, kun ji cewa daya daga cikin manyan mambobin kungiyar ƴan daba ta marigayi Terwase Akwaza da aka fi sani da Gana wanda ya ce sunansa 'Manjo' ya ce za su cigaba da gwagwarmaya duk da shugabansu ya mutu.

Ya ce marigayi Gana ya ji a jikinsa cewa zai mutu hakan yasa ya mika shugabancin ga wanda ke biye masa a ƙungiyar sa kafin zuwa rungumar shirin afuwa filin motsa jiki na Atongo a Katsina-Ala.

Domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel