Yanzu-yanzu: Wani hadimin Gwamna Ortom ya sake mutuwa

Yanzu-yanzu: Wani hadimin Gwamna Ortom ya sake mutuwa

- Mai bawa gwamnan Benue shawara a kan harkokin kananan hukumomi da masarautu Jerome Torshimbe ya mutu

- Torshimbe ya mutu ne a wani asibiti da ke babban birnin tarayya Abuja bayan fama da gajeruwar rashin lafiya kamar yadda majiya daga iyalansa ta ce

- A makon da ta gabata, gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya nada Tershimbe a matsayin shugaban kwamitin yi wa tubabbun masu laifi afuwa na jihar

Mashawarcin Gwamnan Benue, Samuel Ortom a kan harkokin Kananan hukumomi da masarautu, Hon. Jerome Torshimbe ya rasu.

Toshimba ya rasu a yammacin ranar Litinin a wani asibiti da ke Abuja. Ya rasu yana da shekaru 63 a duniya.

Yanzu-yanzu: Wani hadimin Gwamna Ortom ya sake mutuwa
Yanzu-yanzu: Wani hadimin Gwamna Ortom ya sake mutuwa
Asali: Twitter

Wani daga cikin iyalansa ya bayyana cewa ya rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Majiyar ya ce marigayin ya ce yana jin zazabi kuma aka kai shi asibiti a Makurdi daga bisani aka mayar da shi Abuja inda a can ne ya rasu.

DUBA WANNAN: Adamawa: Tsohon gwamnan PDP, Ngillari ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

The Nation ta ruwaito cewa hadimin gwamnan ya jima yana fama da rashin lafiya amma ya ke daure wa yana yin ayyukana.

Ya yi aiki a matsayin tsohon shugaban karamar hukumar Gwer ta Yamma daga 1992 zuwa 1993. Ya kuma rike mukamin kwamishinan Ilimi a karkashin mulkin Sanata Goerge Akume sannan ya yi aiki matsayin direktan yakin neman zaben kujerar Sanata na George Akume a 2011.

KU KARANTA: An kashe ƴan bindiga a Kaduna, an kama ƴan aikensu da N1.5m a Zamfara - Sojoji

A makon da ta gabata, Gwamna Ortom ya nada shi shugaban kwamitin yi wa masu aikata laifuka afuwa da sauya musu halaye.

An gan shi yana ta shige da fice a gidan gwamnatin jihar Benue da ke Makurdi a makon da ta gabata kafin rasuwarsa.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, kun ji wani bakanike da ke Lafia a jihar Nasarawa, John Simon, ya batar da motar kwatomansa a yayin da ya shiga gidan wasu karuwai a sabon yankin Nyanya.

City Round ta gano cewa, Simon na tsaka da shakatawarsa da wata karuwa mai suna Stella Emeerga yayin da wasu mutane uku suka hada kai da ita wurin sace motar kirar Toyota Camry.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel