A wurin caca miji na ya ke kashe dukkan kudinsa: Mata ta nemi kotu ta datse igiyar aurenta

A wurin caca miji na ya ke kashe dukkan kudinsa: Mata ta nemi kotu ta datse igiyar aurenta

- Wata mata ta yi karar mijin ta a kotu tana neman a raba aurensu saboda wai mijin caca ya ke yi da kudadensa

- Matar ta shaidawa kotu cewa mijin ya cika zagin ta da tsinuwa sannan baya kula da ita da yaransu

- A bangarensa, mijin ya musanta abinda matar da fadi inda ya ce ita ce ke kwanciya da maza a waje duk da cewa tana da aure

Wata mata mai sana'ar treda, Fisayo Akibu a ranar Talata ta tafi kotun gargajiya da ke zamansa a Mapo Ibadan tana neman a raba aurenta da mijinta Abiodun saboda yawan yin caca da ya ke yi.

A yayin da ta ke magana gaban alkali, matar mai yara hudu ta ce: "Miji na yana yin caca da dukkan kudin da ya ke samu a maimakon kula da ni da yara na.

A wurin caca miji na ya ke kashe dukkan kudinsa: Mata ta nemi kotu ta datse igiyar aurenta
A wurin caca miji na ya ke kashe dukkan kudinsa: Mata ta nemi kotu ta datse igiyar aurenta. Hoto daga Daily Family
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Adamawa: Tsohon gwamnan PDP, Ngillari ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

"Tunda na auri Abiodun a 2001, bai taba yi wa yara ne bikin suna ba kamar yadda aka saba yi wa yara.

"Bugu da kari, ya kasance yana yawan zagi da yana cewa in bar masa gidansa.

"Don Allah a bani damar in tafi da yarinya ta domin ban gamsu da abinda zai iya faruwa da ita ba idan na bar ta hannunsa."

Abiodun ya shaidawa kotu cewa shima yana goyon bayan a raba aurensu.

Amma ya musanta zargin da ta yi masa a gaban kotun.

KU KARANTA: An kashe ƴan bindiga a Kaduna, an kama ƴan aikensu da N1.5m a Zamfara - Sojoji

"Da gaske ne na samu matsalar kudi a wasu lokuta amma tuni na warware matsalolin.

"Fisayo a shirye ta ke ta yi lalata da duk wani mutum da zai iya bata 'yan kudade kalilan duk da cewa ita matar aure ce.

"Daya daga cikin makwabtan mu mai sana'ar lebura (Baba Oche) ne kwarton ta a yanzu," in ji Abiodun.

Da ya ke yanke hukunci, Shugaban kotun, Cif Ademola Odunade ya raba auren sannan ya bawa matar ikon rike yarsu mace yayin da sauran ukun kuma ya bar wa mijin.

Ya kuma bada umurin Abiodun ya rika biyan N15,000 duk wata a matsayin kudin cin abincin yarsa.

A wani labarin kun ji cewa wani bakanike da ke Lafia a jihar Nasarawa, John Simon, ya batar da motar kwatomansa a yayin da ya shiga gidan wasu karuwai a sabon yankin Nyanya.

City Round ta gano cewa, Simon na tsaka da shakatawarsa da wata karuwa mai suna Stella Emeerga yayin da wasu mutane uku suka hada kai da ita wurin sace motar kirar Toyota Camry.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel