Babur Bura: Takaitaccen tarihi, aure, addini da yaren jama'ar kabilar

Babur Bura: Takaitaccen tarihi, aure, addini da yaren jama'ar kabilar

- Jama'ar kabilar Babur Bura an gano sun fara shigowa kasar nan ne bayan da suka taso daga Yemen

- Sun ratsa ta kasar Sudan da Chadi inda suka shigo Najeriya suka samu matsuguni a Borno, Yobe da Adamawa

- Kamar sauran kabilun kasar nan, suna da addinin da suke yi mai suna Hyel tun kafin zuwan Musulunci ko Kiristanci

Tarihi

Tarihi ya nuna cewa a wani lokaci da ya dade da shudewa, jama'ar sun zo daga Yemen da ke gabas ta tsakiya a kusa da kogin Nil. Har zuwa 600A.D. jama'ar basu watsu ba a duniya, amma da yawansu sun isa Sudan da Sahara.

Abin nazari shine yadda magabatan Babur Bura tare da wasu kabilu kamar Luguda aka yadda cewa sun zo daga kasar Yemen ta Sudan, inda suka ratsa ta tafkin Chadi suka iso jihar Borno da Adamawa ta yanzu.

Ko dai ta yaya suka iso Najeriya, kabilar Babur Bura ana samunsu a jihar Borno a kananan hukumomin Biu, Hawul, Kwaya kusar, Shani da Bayo.

Ana samunsu a jihar Adamawa a kananan hukumomin Garkida a Gombi. Manyan kauyukan Babur Bura da biranensun sune: Biu, Garkida, Kajaffa, Sakwa, Marama, Shaffa, wandali, Kida, Miringa, Buratai, Zuwa, Yimirshika, Hyera, Dayar, Fumwa, Azare, Gwaski, Diragina, Yimana, Gwallam, Tiraku, Shindiffu, Goski, Pela Birni, Wangdand, Bula taw ewe, Kogu Tashn Alade da Hang Shang.

Jama'ar Babur na yawan zama a Biu, kuma nan ne tamkar gida a wurinsu, yayin da jama'ar Bura ke zama a kauyukan da ke kusa. Hakan yasa suka hade ake kiransu da garuruwan Babur Bura.

Aurensu

Kabilar suna da wani tsari na aurar da 'ya'yansu. Idan mace ta haifa diya mace, masoyin diyar kan jefa ganye a bukkarta. Idan mahaifiyar ta amince, za ta karba kuma hakan na nuna za su yi aure idan yarinyar ta girma.

Saurayin kan dinga aiki a gonar mahaifinta kuma ya dinga yin tabarmar Zana har sai ta isa aure. Ya kan shirya abokansa domin dauko masa amaryarsa har gida.

Daga nan sai a fara shirin bikin aure da biyan sadaki wanda ba a kayyade yawansa. A kan kai goro, gishiri da farin yadi.

Ana tsammanin amaryar za ta bada wannan farin yadin bayan sun kwanta da mijinta a ranar farko. Hakan zai sa a tantance ta kai budurcinta ko bata kai ba. Ya kan zama babban abun kunya ga iyayen yarinya matukar ba budurwa bace.

KU KARANTA: Bene ya rushe a Kano, ya kashe yara 2 'yan gida daya, mutum 8 sun jigata

Babur Bura: Takaitaccen tarihi, aure, camfi da yaren jama'ar kabilar
Babur Bura: Takaitaccen tarihi, aure, camfi da yaren jama'ar kabilar. Hoto daga Pulse.ng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Edo 2020: Yadda wanda na gada ya dinga rantowa jihar kudi yana watanda da su - Obaseki

Addini

Kafin zuwan Musulunci da addinin Kirista a 1920, Babur Bura suna da addinin gargajiya wanda suke kira da Hyel ko Hyel-taku.

Suna bauta wa ruwa, duwatsu, tsaunika da dazuzzuka. Su kan yi yanka a ranar Asabar wacce take zama babbar rana ga limamin addininsu wanda suka kira da Mythmaker Haptu.

Yare

Yaren kabilar Babur Bura ya hada yarika kusan uku. Yana yananyi da na Chadi da Biu-Mandara. Kabilar Babur Bura suna da kamanceceniya da jama'ar Chibok, Marghi, Higgi, Kilba da Bazza.

A wani labari na daban, wani babban mallami jami’an Northwest dake jihar Kano, Ferfesa Umar Labdo Muhammad, ya ce asalin jihar Benuwe ta Fulani ce saboda tarihi ya nuna Fulani sun ci jihar Benuwe da yaki.

Ferfesa Umar Labdo Muhammad yace rabin jihar Benuwe mallakar masarutan Bauchi ne kuma sauran rabin yana karkashin jihar Adamawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel