Zaben 2020: Jerin alkawuran da Trump ya cika da wadanda bai cika ba a Amurka

Zaben 2020: Jerin alkawuran da Trump ya cika da wadanda bai cika ba a Amurka

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, na neman tazarce a zaben shugaban kasar da za a gudanar a watan Nuwamba.

A yayin da ya yi kusan shekaru hudu a shugabanci, BBC ta kawo jerin alkawuran da ya yi a lokacin yakin zabensa na shekarar 2016, akwai wadanda ya cika da wadanda bai cika ba.

KARANTA WANNAN: Yan bindiga sun kaiwa jami'an FRSC hari, sun kashe 2, sun sace 10

Zaben 2020: Jerin alkawuran da Trump ya cika da wadanda bai cika ba a Amurka
Zaben 2020: Jerin alkawuran da Trump ya cika da wadanda bai cika ba a Amurka
Source: UGC

Legit.ng Hausa ta kawo jerin alkawuran kamar haka:

Manyan alkawuran da Trump ya cika a cewar BBC:

1. Rage kudaden haraji

A lokacin da ya ke yakin zaben, Shugaba Trump ya yi alkawarin rage harajin da ake tatsa daga kamfanoni, da kuma zabtare harajin da ake tatsa daga ma'aikan kasar.

BBC ta tabbatar da cewa ya cika wannan alkawari, tana nuni da cewa kudurin rage haraji na jam'iyyar Republican 2017 ya samu kammaluwa.

2. Ficewa daga jarjejeniyar yanayi da Farisa

Shugaba Trump ya yi yakinin cewa canjin yanayi wata tatsuwaniya ce da China ta kirkira, kuma ya yi ikirarin cewa yarjejeniyar canjin yanayi da Farisa ya na durkusar da ci gaban Amurka.

KARANTA WANNAN: Mun gaji da zama a Arewa, za mu koma inda muka fito - Kungiyar Yarabawa

Bayan zaman sa shugaban kasa, ya janye Amurka daga wannan yarjejeniya, kuma ficewa daga yarjejeniyar zai fara aiki daga watan Nuwamba, 2020.

3. Nada alkalan kotun koli

Shugaban kasa Trump ya yi alkawarin cewa zai nada alkalan kotun kolin kasar. A halin yanzu dai, ya nada alkalai biyu - Neil Gorsuch da Brett Kavanaugh.

4. Dirkake kungiyar IS

A shekarar 2015, shugaban kasa Trump ya yi gargadin cewa zai dirkake kungiyar ta'addanci ta IS, zai shafe labarinsu.

Ya zuwa yanzu, ya bayar da umurnin hada babban abun fashewa a Amurka, wanda za a aikawa babbar mabuyar kungiyar IS da ke Afghanistan don dirkake su.

5. Canja muhallin ginin jakadancin Amurka da ke Israel

Duk da an samu korafe korafe, a shekarar 2017 Trump ya mayar da ginin jakadancin Amurka zuwa Jerusalem, da ya kalla a matsayin babban birnin Izra'ila.

Manyan alkawuran da Trump ya gaza cikawa a cewar BBC:

1. Mayar da dukkanin bakin haure zuwa kasashensu na asali.

2. Sake yin gine gine da sabunta wadanda suka lalace

3. Gaza cika alkawarin ficewa daga kungiyar NATO

4. Azabtarwa: Trump ya ce zai amince da amfani da tsarin kwarara ruwa a fuskar mutum yayin da aka rufe masa fuska da kyalle, ya ce azabtarwa na horas da masu laifi.

5. Ya gaza yanke hukunci ga Hillary Clinton.

A shekarar 2019, Donald Trump, ya bayyana cewa ya umarci mai bashi shawara a kan harkokin tsaro, John Bolton, da ya yi murabus saboda wasu dalilai banbancin ra'ayi da siyasa.

"Na sanar da John Bolton a daren jiya cewa aikinsa ya kare a 'White House'. Bana iya amince da shawarwarin da yake bashi kan sha'anin da ya shafi tafiyar da gwamnati," cewar Trump.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel