Cacar baki a kan siyan shawarma ya yi sanadin mutuwar wani mutum a Legas

Cacar baki a kan siyan shawarma ya yi sanadin mutuwar wani mutum a Legas

- Wani mutum mai shekaru 35 ya mutu a Legas sakamakon harbinsa da bindiga da wani ya yi a wurin siyan shawarma

- Mutum, Kayode Oloruntoba ya raka abokinsa siyan shawarman ne yayin da wani daban da suka yi cacan baki da abokin ya harbe shi kan kuskure

- Bayan da aka harbe shi, abokansa sun kai shi gidan mai maganin gargajiya aka cire harsashin sannan aka kai shi gida amma daga bisani ya mutu

Ƴan sandan jihar Legas na bin sahun wani mutum da a yanzu ba a gano sunansa ba kan zarginsa da harbin wani Kayode Oloruntoba a jikinsa a wurin cin abinci da ke Alagbado na Legas a ranar Juma'a.

Mutane sun yi ƙoƙarin ceto rayuwar Oloruntoba ciki har da abokinsa Kazeem Okikiola amma ba su yi nasara ba domin ya rasu.

Cacar baki a kan siyan shawarma ya yi sanadin mutuwar wani mutum a Legas
Cacar baki a kan siyan shawarma ya yi sanadin mutuwar wani mutum a Legas. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gana ya san zai mutu, ya nada wanda zai gaje shi

Punch metro ta ruwaito cewa a ranar Juma'a 11 ga watan Satumba Okikiola ya tafi Avid Bar da ke Alagbado a Legas don siyan shawarma kuma ya kira abokinsa Oloruntoba ya ce ya same shi a can.

A lokacin da ya ke jiran Shawarman, rikici ya barke tsakanin Okikiola da wani kwastoma da shima ya zo siyan shawarman.

Suna rikici ne a kan wanda ya riga zuwa hakan yasa wanda ake zargi da kisar ya fusata ya shiga motarsa ya tafi.

Bayan ƴan mintoci kaɗan Oloruntoba ya iso wurin ya tarar da abokinsa Okikiola kuma a lokacin da suke jiran Shawarman sai wanda ake zargin ya dawo ya harbe su da bindiga.

Harsashin bindigan ta samu Oloruntoba a ciki yayin da wanda ake zargin ya tsere nan take.

Wani mazaunin unguwar, Chinedu ya ce wanda ake zargin ya harbe mutumin mai shekaru 35 da kuskure.

KU KARANTA: An sace motar da aka bawa bakanike gyara yayin da ya tafi gidan karuwai da motar

"Ya yi tunanin ya harbi wanda suka yi rikici tare ne wato Okikiola. Amma bai sani ba harsashin ta harbi wani daban. Nan take ya shige motarsa ya tafi," in ji shi.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Olumuyiwa Adejobi ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce suna yiwa wasu mutum shida da ake zargi tambayoyi ciki har da Okikiola.

Adejobi ya ce bayan harbin abokansa ba su shigar wa yan sanda rahoto ba amma suka kai shi wurin mai maganin gargajiya inda ya ciro harsashin daga cikinsa kuma daga bisani suka kai shi gida inda ya mutu.

Kwamishinan ƴan sandan na jihar CP Hakeem Odumosu ya umurci sashin binciken manyan laifuka CID su zurfafa bincike a kan lamarin.

A wani labarin daban, kun ji cewa Jarumin Bollywood Akshay Kumar ya bayyana cewa a kullum ya kan sha fitsarin shanu domin kiyayye kansa daga kamuwa daga cutar korona.

Jarumin ya shiga sahun mutane da dama a Indiya da suka yi imanin cewa fitsarin shanun na maganin Coronavirus.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel