Da duminsa: Ganduje, Yahaya Bello, da Oshiomole na cikin mutanen da Amurka ta haramtawa shiga kasarta

Da duminsa: Ganduje, Yahaya Bello, da Oshiomole na cikin mutanen da Amurka ta haramtawa shiga kasarta

- Gwamnatin kasar Amurka ta lashi takobin karfafa Demokradiyya a Najeriya

- Gudunmuwar da zata iya badawa shine sanyawa duk wanda aka samu da magudi takunkumi

- Da dama daga cikin yan siyasan Najeriya na da gidaje da dukiya a Amurka

Tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban uwar jam'iyyar All Progressives Congress, Adams Oshiomhole, na cikin wasu jiga-jigan siyasa a Najeriya da gwamnatin Amurka ta haramtawa shiga kasarta saboda zargin magudin zabe.

A ranar Litinin gwamnatin Amurka ta sanar da cewa ta haramtawa wasu yan siyasa a Najeriya shiga kasarta daga yanzu saboda zargin rashawa ko magudin zabe.

Rahoton da Sahara Reporters ta wallafa ya kara da cewa akwai sunan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje; da gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.

Shi kuma gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, an tsawaita haramtawar da akayi masa tun a baya.

A cewar jami'an kasar Amurka, za'a kara sunayen wasu yan siyasan Najeriya cikin jerin wadanda aka haramtawa shiga kasar bayan zaben jihar Edo idan sukayi magudi.

An samu labarin cewa an turawa yan siyasan da aka haramtawa sakonnin akwatin email ko na waya.

Da duminsa: Ganduje, Yahaya Bello, da Oshiomole na cikin mutanen da Amurka ta haramtawa shiga kasarta
Da duminsa: Ganduje, Yahaya Bello, da Oshiomole na cikin mutanen da Amurka ta haramtawa shiga kasarta
Source: Twitter

A ranar Litinin, Gwamnatin Amurka ta ce ta saka wa wasu mutane takunkumi hana su shigar ƙasar ta saboda magudin zabe da suka yi yayin zabukkan gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa da aka yi a 2019.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake shirin yin zabukkan gwamnoni a jihohin Edo da Ondo a watan Satumba da Oktoba na 2020.

Duk da cewa ba a riga an yi zabuka a Edo da Ondo ba, Sakataren Gwamnatin Amurka Mike Pompeo ya ce akwai wasu da aka haramta musu shiga kasar ta Amurka.

Hakan na cikin wata sanarwa ne mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun ma'aikatar wajen Amurka, Morgan Ortagus da ya fitar a ranar Litinin.

"A watan Yulin 2019, mun sanar da haramta wa wasu ƴan Najeriya da suka yi magudin zabe a zabukkan Fabrairu da Maris na 2019 shiga kasar mu.

"A yau, Sakataren Gwamnati ya ƙara saka takunkumin a kan wasu mutane saboda abubuwan da suka aikata da ke da alaƙa da zaɓukkan da aka yi a Nuwamban 2019 a jihohin Kogi da Bayelsa da kuma zabukkan da ke tafe a watannin Satumba da Oktoban 2020 a jihohin Edo da Ondo."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel