Zulum zai dauki ma'aikatan lafiya 594 a fadin jihar Borno

Zulum zai dauki ma'aikatan lafiya 594 a fadin jihar Borno

- Gwamnatin jihar Borno karkashin mulkin gwamna Babagana Zulum ta bada sanarwar daukar ma'aikata kusan mutum dari shida a fadin jihar

- Gwamnatin za ta dauki ma'aikatan domin karawa akan wadanda suke aiki a yanzu, domin tabbatar da kula da marasa lafiya a jihar

- Zulum ya bayyana hakane a jiya bayan wani taro da ya halarta a gidan gwamnatin jihar dake garin Maiduguri babban birnin jihar

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da daukar ma'aikatan lafiya kimanin mutum 600 a jihar, wadanda za su dinga aiki a asibitocin jihar baki daya.

Ma'aikatan sun hada da kwararrun likitoci guda 84, likitoci mata da ingozomomi guda 365, masu bada magani guda 45, sai kuma masu lura da asibiti da sauran ma'aikata mutum 100, inda jimillarsu suka zama mutum 594.

Zulum zai dauki ma'aikatan lafiya 594 a fadin jihar Borno
Zulum zai dauki ma'aikatan lafiya 594 a fadin jihar Borno | Source: Facebook
Asali: Twitter

Gwamnan ya bayyana daukar ma'aikatan ne a jiya Litinin 14 ga watan Satumba a garin Maiduguri babban birnin jihar, bayan kammala taro da masu ruwa da tsaki na fannin lafiya a jihar.

KU KARANTA: Saurayi ya tura wa budurwa N50,000 saboda damar hira da ita da ta bashi a kafar sada zumunta

Taron ya samu halartar shugaban kwamitin lafiya ta jihar Borno, kwamishinan lafiya, Dr Salihu Kwayabura, shugaban kungiyar ingozomomi na jihar Borno, Umar Shettima, da kuma shugaban kula da bangaren lafiya na jihar Borno, da dai sauransu. An gabatar da taron a gidan gwamnatin jihar.

KU KARANTA: Kaduna: Ambaliyar ruwa ta lashe rayuka 3, gidaje da yawa sun salwanta

Zulum ya bayyana cewa ingozomomi 365 da za a dauka duka sababbin ma'aikata ne da suka gama kwaleji. Sauran kuma an daukesu saboda kwarewarsu, wasu ma sun jima da yin ritaya daga aiki a jihar Borno.

Haka kuma bayan shekaru shida da sace sama da dalibai 200 a makarantar mata ta Chibok, an gabatar da jarrabawar kammala sakandare ta WAEC a karon farko a garin.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa makarantun sakandare na Chibok dake jihar Borno an basu damar gabatar da jarrabawar ta WAEC.

Legit.ng ta gano cewa wani babban jami'in hukumar soja ne mai suna Abdul-Khalifa Ibrahim, ya bayyana haka a lokacin da yake karbar bakuncin ziyarar wasu mambobi na kungiyar ilimi mai suna (EiEWG) a ranar Alhamis, 10 ga watan Satumba, a garin Maiduguri, jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel