Matar da tace takalmi yafi kanin mijinta daraja tayi dana sani bayan yayi kudi yayi mata goma ta arziki

Matar da tace takalmi yafi kanin mijinta daraja tayi dana sani bayan yayi kudi yayi mata goma ta arziki

- Wani dan Najeriya ya bayyana yadda matar yayanshi da ya rasu ta dinga gallaza masa

- Mutumin wanda yake da suna @Omodenden1 a shafin Twitter, ya bayyana cewa matar yayansan ta taba cire takalmi, ta nuna kasan takalmin tace masa kasan takalmin ya fishi daraja

- Mutumin ya bayyana cewa yanzu haka ya zama lauya, kuma shine yake lura da 'ya'yanta

Wani saurayi dan Najeriya ya hau shafinsa na Twitter, ya bayyana yadda matar yayansa da ya mutu ta takurawa rayuwarsa shekaru 20 da suka wuce, a lokacin da yake zaune da su.

Mutumin wanda yake da suna @Omodenden1 ya bayyana wannan rayuwa da ya fuskanta a baya a shafin nasa a matsayin sharhi da ya yiwa wani mai suna Segun Awosanya.

Awosanya da yake da suna @segalink ya shawarci mutane da su daina cin mutuncin mutane 'yan uwansu.

Matar da tace takalmi yafi kanin mijinta daraja tayi dana sani bayan yayi kudi yayi mata goma ta arziki
Hoton saurayin da aka cewa takalmi yafi shi daraja: Source: Twitter Page
Source: Twitter

Ya ce: "Ku daina yiwa mutane izgilanci da kuma raina su. Allah ne yake da ikon yin duk abinda yake so da mutum. Shine yake da ikon mayar da duk wani wanda yake so ya zama wani a rayuwa. Idan halinka ne zaka sha wahala a rayuwa. Babu abinda zai ragu a tare da kai dan ka yiwa mutum kirki."

KU KARANTA: Budurwa ta rayu bayan ta fado daga bene mai hawa 8, yayin da take gujewa saurayinta

Wannan rubutu ya sanya @Omodenden1 ya shiga bangaren sharhi ya bayyana halin da ya shiga a rayuwar da yayi a baya.

Ya ce matar yayanshi wanda ya mutu ta cire takalmin kafarta ta nuna shi da shi ta bayyana mishi cewa wannan takalmi yafi shi daraja a wajenta.

Ya ce yanzu ya zama lauya kuma shine yake daukar nauyin dan data haifa. Ya ce yanzu matar tana jin kunyar tinkarar shi, sai dai ta dinga turo wakili idan za ta yi magana da shi.

A cewar shi: "Kimanin shekaru 20 da suka wuce, matar yayana da nake zaune da ita ta taba cire takalminta, ta nuna ni da shi ta ce takalminta ya fini daraja. Yanzu kuma yayana ya mutu. Na zama lauya, kuma nine nake lura da danta. Amma ta kasa tinkara ta, sai dai ta turo dan aike idan tana son magana dani."

KU KARANTA: Bidiyon wajen da aka binne marigayi Sanata Ajimobi da aka cika wajen da kayan alatu, da wutar lantarki wacce bata daukewa

Ita kuwa wata mata da ta fito daga yankin Embakasi mai suna Shamim ta bayyana dalilan da ya sanya baza ta yafewa mijinta ba.

A wata hira da tayi da wani mai suna Anthony Ndiema a wani shiri mai suna Nisamehe Show, matar ta bayyana cewa mijinta ya zabga mata karya wacce ta kasa hakuri da shi bayan ta gano gaskiya.

Shamim ta bayyana cewa ita abinda ta sani shine mijinta ma'aikacin filin jirgin sama ne, har zuwa lokacin da ta hadu da makwabtanta a lokacin ne ta gano gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel