Yanzu yanzu: Allah ya yiwa Sarkin Biu, Mai Umar, rasuwa

Yanzu yanzu: Allah ya yiwa Sarkin Biu, Mai Umar, rasuwa

- Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un

- Cikin shekarar nan, jihar Borno ta sake rashin wani Basarake

- Alhaji Mai Umar ya yi shekaru 31 kan karagar mulkin masarautar Biu kafin rasuwarwa

Allah ya yiwa mai martaba Sarkin masarautar Biu a jihar Borno , Alhaji Mai Umar Mustapha Aliyu, rasuwa yana mai shekaru 79.

Ya rasu a daren Litinin a asibitin gwamnatin tarayya dake Gombe, bayan gajeruwar rashin lafiya.

A cewar Iyalan marigayin, sun bayyana cewa: "Mun yi rashin ginshikin masarrautar Biu da jihar Borno gaba daya, Sarkin Biu.”

”Allah ya gafarta kura-kuransa kuma ya azurtashi da gidan Aljannah Firdawsi mafi girma.”

Alhaji Mai Umar Mustapha Aliyu ya hau mulkin masarautar ne a shekarar 1989.

KU KARANTA WANNAN: Shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Bama (Hotuna)

Yanzu yanzu: Allah ya yiwa Sarkin Biu, Mai Umar, rasuwa
Yanzu yanzu: Allah ya yiwa Sarkin Biu, Mai Umar, rasuwa
Source: Twitter

Bayan rasuwar Shehun Bama, Alhaji Kyari El-Kanemi, Gwamna Babagana Zulum ya nada sabon sarki a Bama.

Amma a yau Asabar, 9 ga watan Mayun 2020 aka yi bikin nadin sarautar sabon sarkin Alhaji Umar Ibn Kyari El-Kanemi.

DUBA NAN: Zulum zai dauki ma'aikatan lafiya 594 a fadin jihar Borno

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel