Hotuna: EFCC ta damke malaman jami'a 2 da wasu 28 a kan damfara
- Hukumar EFCC reshen jihar Kwara ta kama wasu malaman kwalejin kiwon lafiya 2 da wasu mutum 28 a akan zargin damfara
- An kama su sakamakon bayanan sirri da EFCC ta samu game da miyagun ayyukansu a fadin jihar Kwara
- An samo motoci, wayoyi da na'urori masu kwakwalwa daga wurinsu, amma ba a kama bokan da ke da alaka da su ba
Jami'an hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), da ke Ilorin sun damke malaman kwalejin kiwon lafiya da ke Kwara guda biyu, tare da wasu mutum 28 a kan zargin damfarar yanar gizo.
Malaman makarantar sune: Abdulahi Opashola da Adebisi Ademola. Sauran mutum 28 da aka kama kuma ake zargi sune: Kingsley Essien; Tobiloba Adenuga; Tope Ayodele; Rasheed Mujib; Oladipo Opeyemi; Saadu Muktar; Oladejo Hammed; Hammed Tope; Ameachi Umenyi, Salauden Adam da Afolabi Gafar.
Sauran sun hada da: Oladimeji Timi; Remilekun Adeolu; Audu John; David Momodu; Abdulkareem Samad; Adebiyi Sodiq; Dawodu Olusoji; Yusuf Amoo; Kehinde Olarenwaju; Philip Mike, Ademola Adebukola da Adeniyi Olamilekan.
Ragowar sune: Adeyemi Adedeji; Ajayi Teslem; Olawale Oladayo, Olasunkanmi Olawale da Adeleke Damilola.
An kama su a wurare daban-daban a cikin jihar Kwara bayan bayanan da jami'an suka samu a kan laifukan da suke aikawata.
A halin yanzu, ana kokarin kama bokan da ke da alaka da su, Channels TV ta tabbatar.
Kayayyakin da aka samu daga wurinsu sun hada da motoci, wayoyi da nau'rori masu kwakwalwa.
KU KARANTA: Saurayi ya tura wa budurwa N50,000 saboda damar hira da ita da ta bashi a kafar sada zumunta
KU KARANTA: Masoya sun sha maganin kwari, sun sheka lahira bayan an hana su aure
A wani labari na daban, jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya sun kama wasu mutane guda goma ranar Larabar nan da ta gabata da ake zargin 'yan damfara ne na yanar gizo, a wata maboyarsu dake Sapele, jihar Delta.
Kama 'yan damfarar ya biyo bayan sakonnin sirri da hukumar EFCC din ta samu akan maboyar 'yan damfarar, inda suka yi musu dirar mikiya a safiyar ranar Larabar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng