Kaduna: Ambaliyar ruwa ta lashe rayuka 3, gidaje da yawa sun salwanta

Kaduna: Ambaliyar ruwa ta lashe rayuka 3, gidaje da yawa sun salwanta

- Rayuka uku aka rasa yayin da gidaje masu tarin yawa suka salwanta a karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna

- Ambaliyar ruwa da aka yi sakamakon mamakon ruwan saman da aka yi daga ranar Alhamis zuwa Juma'a ne ya kawo hakan

- Sakataren hukumar taimakon gaggawa ta jihar, Abubakar Hassan, ya ziyarci yankunan da lamarin ya shafa

Wasu yankuna na karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun fuskanci ambaliyar ruwan sama wanda ya janyo mutuwar rayuka uku tare da salwantar gidaje masu tarin yawa.

Ambaliyar ruwan ta faru ne sakamakon gagarumin ruwan saman da aka yi daga ranar Alhamis zuwa Juma'a a yankunan da lamarin ya shafa.

Wasu daga cikin yankunan da abun ya shafa sun hada da Hunkuyi, Likoro da Kudan duka a jihar Kaduna, The Punch ta wallafa.

Da yawa daga cikin mazauna yankin sun koma basu da matsuguni saboda mamayewar da ruwa yayi wa nasu.

Babban sakataren hukumar taimakon gaggawa ta jihar, Abubakar Hassan, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Hassan, wanda ya ziyarci yankunan, ya danganta aukuwar lamarin da yadda aka dinga gine-ginen yankin a hanyoyin ruwa ko kuma kusa da tafkuna.

Cibiyar a ranar Alhamis ta ja kunnen mazauna yankunan da ke kusa da ruwa da su bar yankunan domin tare da komawa wasu sassa na jihar.

KU KARANTA: Kishi: Matashi ya kashe tsohuwar budurwarsa bayan ya dade sanar da jama'a zai kasheta

Kaduna: Ambaliyar ruwa ta lashe rayuka 3, gidaje da yawa sun salwanta

Kaduna: Ambaliyar ruwa ta lashe rayuka 3, gidaje da yawa sun salwanta. Hoto daga Punch
Source: Facebook

KU KARANTA: Ndume ya jinjiinawa rundunar sojoji a kan samar da tsaro da tallafi

A wani labari na daban, Hukumah bada agajin gaggawa ta jihar Jigawa, SEMA, ta sanar da cewa yawan mutanen da suka mutu ya kai 2 tare da dubban gidaje da gonakin da suka lalace sakamakon gagarumar ambaliyar da ta auku a jihar.

hukumar, Mr Yusuf Sani Babura, ya sanar wa manema labarai a Dutse cewa ambaliyar, wanda ke aukuwa duk shekara, ya shafi 17 daga cikin kananan hukumomi 27 na jihar wanda hakan ya jefa rayukan jama'a mazauna garuruwan cikin rudani.

kara da cewa mafi yawar wanda suka rasa rayukan su yara ne kanana sakamakon rugujewar gine gine

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel