Masoya sun sha maganin kwari, sun sheka lahira bayan an hana su aure

Masoya sun sha maganin kwari, sun sheka lahira bayan an hana su aure

- Wasu masoya biyu 'yan asalin kabilar Ibo sun sha maganin kwari inda suka sheka lahira

- Kamar yadda suka sanar a takardar da suka bari, iyayensu sun hana su aure saboda daya daga ciki na daga tsatson bayi

- Wannan al'adar a kasar Ibo ta dade tana hana masoya cimma burikansu na kasancewa tare

Wadansu masoya biyu da ke Okija a jihar Anambra sun kashe kansu a farkon watan Satumba, sakamakon hana su aure da aka yi saboda daya daga cikinsu na daga tsatson bayi.

Kamar yadda BBC ta wallafa, masoyan suna cikin shekarunsu na talatin, kuma suna kokarin yin aure yayin da iyayensu suka soki lamarin.

A wata takarda da suka bari, masoyan sun soki yadda aka hana su auren juna saboda wata tsohuwar al'ada da camfi.

"Sun ce ba za mu iya aure ba saboda wata tsohuwar al'ada da camfi," suka rubuta.

"Ubangiji ya halicci kowa kuma duka daya ake. A kan mene dan Adam zai kawo banbance-banbane saboda wani jahilci na magabatanmu."

Kamar yadda wadannan masoyan suka fuskanci kalubale, akwai jama'a masu tarin yawa da ke fuskantar matsala saboda suna da tsatson bayi a kabilar Ibo da ke yankin kudancin Najeriya.

Masoyan sun sha maganin kwari, sun sheka lahira bayan an hana su aure

Masoyan sun sha maganin kwari, sun sheka lahira bayan an hana su aure. Hoto daga The Cable
Source: Twitter

KU KARANTA: Sabon harin 'yan bindiga: Mutum 2 sun rasu, an kone gidaje masu yawa a Kaduna

KU KARANTA: Jerin sunaye: Buhari ya yi sabbin nade-nade a bangaren wutar lantarki

Tsatson bayi sun fada kashi biyu a kabilar Ibo. Sune Ohu da Osu. Tsatson Ohu ya fito daga jama'a wadanda aka mallaka, ma'ana bayi. Osu kuwa daga ababen bauta ne, sune suka mallakesu.

Wadanda ke da alaka da wadannan tsatson ana hana su auren sauran 'yan kabilar Ibo, kuma ana haramta musu rike kowanne mukami na siyasa.

A wani labari na daban, wani matashi mai shekaru 30 ya shiga hannun jami'an tsaro a hammanskraal, yankin arewacin Pretoria sakamakon zarginsa da ake da soka wa tsohuwar budurwarsa wuka har ta mutu.

Matashin ya kashe tsohuwar budurwarsa har lahira bayan ta yi sabon saurayi, kamar yadda jami'an 'yan sandan yankin Guateng suka sanar a ranar Lahadi 13 ga watan Satumban 2020.

Matashiyar mai shekaru 23 ta matukar shan wahala sakamakon sossoka mata wuka da tsohon saurayinta yayi bayan kwashe dongon lokacin da yayi yana sanar da jama'a cewa sai ya kasheta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel