Mbappe ya bawa kungiyar PSG takardar bankwana, zai koma wata kungiya a Ingila

Mbappe ya bawa kungiyar PSG takardar bankwana, zai koma wata kungiya a Ingila

- Dan wasan gaba na kasar Faransa, Kylian Mbappe, ya sanar da kungiyar PSG cewa zai barsu a karshen kakar wasannin bana

- Mbappe ya nuna sha'awarsa ta komawa kungiyar Liverpool ko Manchester United a kasar Ingila

- Ana ganin sauran manyan kungiyoin kwallon kafa na duniya za su shiga zawarcin dan wasan duk da ya fi son taka leda a kasar Ingila

Kylian Mbappe ya bawa kungiyar PSG da mahukuntanta mamaki bayan ya sanar dasu cewa zai bar kungiyar a karshen kakar wasannin bana.

Mbappe, dan wasan gaba a kungiyar PSG da kasar Faransa, yana shirin girgiza duniyar kwallon kafa bayan ya nuna alamun cewa zai koma kungiyar Manchester United ko Liverpool a kasar Ingila.

Ma su nazarin harkokin wasanni sun bayyana cewa manyan kungiyoyin kwallon kafa irinsu Barcelona da Real Madrid za su shiga zawarcin dan wasan duk da ya nuna cewa Ingila ya ke son komawa.

A shekarar 2018 ne kungiyar PSG ta sayi Mbappe a kan Yuro miliyan dari da hamsin da biyar (E165m) kuma har yanzu da sauran shekara biyu a kwantiraginsa.

A cewar jaridar The Times, Mbappe ya sanar da PSG cewa zai dan jinkirta barin kungiyar domin basu damar tattara kudin sauyin kungiyar da zai yi.

Duk da ya nuna sha'awarsa a kan salon taka leda na kungiyar Liverpool a karkashin mai horarwa, Jurgen Klopp, Mbappe ya bayyana cewa yana sha'awar taka leda a kungiyar Manchester United.

Mbappe ya bawa kungiyar PSG takardar bankwana, zai koma wata kungiya a Ingila
Kylian Mbappe
Asali: Getty Images

"Kungiyar Liverpool na matukar burgeni a wannan lokacin," kamar yadda Mbappe ya bayyana a watan Janairu.

"Su na taka leda kamar su na aiki da inji a jikinsu, su na samun karfin gwuiwa daga kasidun goyon baya da yabo da magoya bayansu ke rerawa duk lokacin da su ke wasa.

DUBA WANNAN: Bidiyo: Rundunar yan sanda ta fara farautar jami'inta da aka nuna yana shan shisha

DUBA WANNAN: Kakar wasanni ta Premier: Matasan 'yan wasa biyar masu tashe a taka leda

"Za ka dauka wasan kwallo ya na da sauki yayin da ka ke kallon wasa da kungiyar Liverpool, amma na san babu sauki.

"Sun shirya sosai, sun mayar da hankali a wasannin da su ke bugawa, hakan ya sa su na samun nasara a wasanninsu.

"Salon wasansu ya nuna cewa su na yin atisaye sosai kuma sun samu kociya mai nagarta, wanda ya san aiki," a cewar Mbappe yayin magana a kan kungiyar Liverpool.

A wani labarin, A ranar Asabar ne aka fara kakar wasanni ta Premier ta wannan shekarar, tare da wasu matasan 'yan wasa, da su ka fara tashe a wasan na taka leda.

Bayan da dan wasan Manchester United Mason Greenwood ya zamo dan wasa mai tashe a kakar bara, jaridar Legit.ng Hausa ta duba wasu 'yan wasa biyar da za su yi tashe a kakar wasan bana.

Yan wasan sune: Phil Foden (Manchester City), Kalvin Phillips (Leeds), Bukayo Saka (Arsenal), Matheus Pereira (West Bromwich Albion) da kuma Curtis Jones (Liverpool).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel