Yanzu-yanzu: Motar haya ta yi kicibis da motar 'Daf', an rasa rayuka (Bidiyo)

Yanzu-yanzu: Motar haya ta yi kicibis da motar 'Daf', an rasa rayuka (Bidiyo)

An yi mumunar hadari a hanyar Enugu zuwa Abakaliki tsakanin wata motar DAF da wata motar haya cike da fasinjoji.

Rahoton TVC ya nuna cewa an yi rashin akalla rayuka 10.

Faifan bidiyo ya nuna gawawwakin wadanda hadari ya shafa da kuma mutane suna kokarin fito da su la'alla za'a samu wanda ya rayu.

A wani labarin ranar Litinin, Wata mota dauke da fasinjoji har shida ta ci karo da jirgin kasa da ke tafiya dauke da fasinjoji a Oshodi da ke jihar Legas.

Darakta janar na hukumar taimakon gaggawa (LASEMA), Olufemi Oke-Osanyintolu ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce motar hayan ta haye dogon, inda ta ci karo da jirgin mai tafiya, gidan talabijin na Channels TV ya ruwaito.

Karin bayani na nan tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel