Gamayyar dattawa da matasan Arewa mazauna jihar Edo sun alanta goyon bayansu Osaze Ize-Iyamu (Hotuna da Bidiyo)

Gamayyar dattawa da matasan Arewa mazauna jihar Edo sun alanta goyon bayansu Osaze Ize-Iyamu (Hotuna da Bidiyo)

- Yayinda Kwankwaso ke yiwa PDP yaki, Shekarau na nasa yakin wa APC a Edo

- Sarkin Hausawan jihar Edo ya alanta goyon bayansa ga dan takaran APC

Gamayyar dattawa da matasan Arewa mazauna jihar Edo bayyana goyon bayansu ga dan takarar kujeran gwamnan jihar karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC, Fasto Osaze Ize-Iyamu, TVC ta ruwaito.

Hakan ya gudana ne yau Asabar, 12 ga watan Satumba, 2020 yayinda Sanata Ibrahim Shekarau yake jihar domin yiwa APC yakin neman zabe.

Tsohon gwamnan jihar Kanon ya tafi jihar Edo ne domin janyo hankalin Hausawa mazauna jihar su zabi dan takaran jam'iyyar APC, Ize-Iyamu.

Legit ta samu labarin cewa a ranar Juma'a, Malam Ibrahim Shekarau ya gana da al'ummar Arewan karkashin jagorancin Sarkin Hausan Benin, Alhaji Adamu Isah Dutse.

Hakazalika ya gana da kungiyar matan arewa mazauna Edo, karkashin jagorancin Hajiya Altine.

Gamayyar dattawa da matasan Arewa mazauna jihar Edo sun alanta goyon bayansu Osaze Ize-Iyamu (Hotuna da Bidiyo)

Edo/Shekarau
Source: Facebook

KU KARANTA NAN: Yan bindiga sun shiga dajin Falgore a jihar Kano - Rahoto

Gamayyar dattawa da matasan Arewa mazauna jihar Edo sun alanta goyon bayansu Osaze Ize-Iyamu (Hotuna da Bidiyo)

Edo/Shekarau
Source: Facebook

Bidiyo:

A bangare guda, wasu gungun mutanen Arewa da ke zaune a jihar Edo sun tabbatar da goyon bayansu ga tazarcen mai girma Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP.

Sakataren mai girma Sarkin Hausawan Benin, Mohammed Baba, ya bayyana cewa kuri’arsu ta na wurin PDP a zaben gwamnan da za ayi a jihar Edo.

Jaridar Vanguard ta ce wadannan Hausawa da ke zaune a garin Benin sun ce, “Ba mu da zabi illa mu goyi bayan PDP a zaben 19 ga watan Satumban 2020.”

“Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, Jakadanmu ne. Ya fada mana mu zabi Gwamna Obaseki, kuma hakan za mu yi.” Inji Mohammed Baba.

Game da wannan ra’ayi, sakataren shugaban Hausawan ya bayyana cewa su na daukar Sanata Kwankwaso a matsayin Jagorarsu, kuma su na girmama shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel