Kada ku sassauta wa 'yan bindiga: Huɗubar Buratai ga sojojin Najeriya

Kada ku sassauta wa 'yan bindiga: Huɗubar Buratai ga sojojin Najeriya

- Shugaban sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya zaburar da sojojin rundunar Operation Sahel Sanity da ke yaki da 'yan bindiga

- Buratai ya ce kada su rika sassauta wa ko tausayawa yan bindigar ko kadan a yakin da suke yi na kawar da miyagu a yankin

- Buratai ya yi wannan kirar ne yayin da ya kai ziyara sansanin sojoji da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina

Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, a ranar Asabar ya bukaci sojojin Opertion Sahel Sanity su ragargaji 'yan bindiga da sauran miyagu ba tare da tausayi ko sassauci ba.

Ya ce rundunar sojojin ba za ta bawa masu aikata laifuka damar su numfasa ba kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kada ku sassauta wa 'yan bindiga: Hudubar Buratai ga sojojin Najeriya

Kada ku sassauta wa 'yan bindiga: Hudubar Buratai ga sojojin Najeriya. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An sace motar da aka bawa bakanike gyara yayin da ya tafi gidan karuwai da motar

Buratai ya yi wannan jawabin ne a sansanin sojoji da ke karamar hukumar Faskari na jihar Katsina a yayin da ya kai ziyarar duba yadda aikin rundunar Operation Sahel Sanity da aka kaddamar a Arewa maso Yamma ke tafiya.

Ya kara da cewa rundunar soji tana da karfin da za ta iya magance yan bindigar da kuma dawo da doka da oda a yankin arewa maso yamma da sauran sassan Najeriya baki daya.

Ya yi kira ga mutane su dena bawa masu laifi mafaka domin wata rana za su juya musu baya.

"Miyagun da ke aikata laifuka suna cikin al'ummar da ke neman kariya kuma suna da kanai, yayyi da sauran dangi domin ba daga sama suka fado ba.

KU KARANTA: An kama wani da yayi shekaru 2 yana karbar albashin kwamishina a Niger

"Da zarar mutane sun dena boye masu laifi, za mu samu damar kawar da laifuka cikin gaggawa a garuruwan mu.

"Duk da haka, muna da sabbin na'urorin zamani na tattara bayannan sirri kuma dai mutane suna kara bada hadin kai.

"Idan mutane suna kokwanto na tona asirin miyagu da ke cikinsu, su sani cewa a shirye mu ke mu saurare su.

"Miyagun za su juya wa 'yan uwansu baya wata rana.

"Miyagun suna nan suna yawo cikin gari kuma idan har ana son samar da tsaro a garuruwan mu, sai an tona asirin su," in ji shi.

A wani labarin daban, fitaccen malamin addinin musulunci mazaunin Kano, Nasidi Goron-Dutse ya koka a kan rayuwar ƙunci da ƴan Najeriya ke ciki musamman musulmi.

Duk da cewa malamin bai ambaci sunan Shugaba Muhammadu Buhari ba, ya nuna damuwarsa a kan yadda wahalhalu, hauhawan farashin kaya da rashin aikin yi ke ƙaruwa a ƙasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel