Gana ya san zai mutu, ya nada wanda zai gaje shi

Gana ya san zai mutu, ya nada wanda zai gaje shi

- Wani daga cikin ƴan kungiyar yan daba na Gana da ke Benue ya ce narigayin ya riga ya zaɓi magajinsa kafin ya mutu

- Ya ce Gana ya ji a jikinsa cewa ba dole ne ya dawo da rai ba hakan yasa ya zaɓi wanda zai maye gurbinsu

- Wanda ya maye gurbin Gana mai suna Manjo ya ce gwagwarmayar da tsohon shugaban su ya fara ba za ta tsaya ba

Ɗaya daga cikin manyan mambobin kungiyar ƴan daba ta marigayi Terwase Akwaza da aka fi sani da Gana wanda ya ce sunansa 'Manjo' ya ce za su cigaba da gwagwarmaya duk da shugabansu ya mutu.

Ya ce marigayi Gana ya ji a jikinsa cewa zai mutu hakan yasa ya mika shugabancin ga wanda ke biye masa a ƙungiyar sa kafin zuwa rungumar shirin afuwa filin motsa jiki na Atongo a Katsina-Ala.

Gana ya san zai mutu, ya nada wanda zai gaje shi
Gana ya san zai mutu, ya nada wanda zai gaje shi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An sace motar da aka bawa bakanike gyara yayin da ya tafi gidan karuwai da motar

Manjo wadda ya ce asalin sunansa Aondehembe a hirar da ya yi da The Nation a Keffi a ranar Juma'a da yamma a hanyarsa na zuwa Abuja yi wa matar marigayin jaje.

"Mun masa gargadi, mun faɗa masa cewa dabara suke masa don ya fito, ya yarda da mu amma ya ce ya riga ya yanke ya yanke hukunci kuma ya gaji da zama a daji."

"Ya faɗa mana cewa zai fito daga daji ne don karrama Bishop ɗin Gboko, William Aveyam da Sanata Gabriel Suswam da suka dade suna matsa masa ya rungumi zaman lafiya."

KU KARANTA: Bidiyo: Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Goron-Dutse

Ya ce Gana ya basu horo kuma sun kai kimanin 200 a jihar Benue da Taraba, "Bataliya muke da shi, muna da tsari mai kyau, Gana shugaba ne da ke ƙaunar mu.

"A ranar da abin ya faru ya tara mu da safe ya faɗa mana abinda za muyi idan har bai dawo da rai ba, ya ce idan har an kashe shi mu cigaba da gwagwarmaya amma idan da gaske ne afuwar mu ajiye makaman mu," in ji shi.

Ya ce Bishop Aveyam ya kan kira Gana a waya yana masa wa'azi kuma ya tuba har yana shirin zai tafi coci ya auri matarsa.

"Ina cikin mutum biyar suka tsere da sojoji suka tsayar da motar mu a Gboko a hanyar mu ta zuwa Makurdi.

"Gana bai tsere ba domin ya riga ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa kafin ya kama hanya zuwa Makurdi."

Ya ce Gana ya rasu amma gwagwarmayarsu ba za ta tsaya ba domin ya riga ya bayar da wasiyyar abinda za a yi bayan ya mutu.

A wani labarin daban, kun ji cewa, Rundunar Ƴan sandan jihar Katsina sun kama wani hatsabibin mai garkuwa da mutane, Abubakar Ibrahim a dajin Rugu da ke jihar.

An kuma ceto mutum uku da ya yi garkuwa da su bayan kama mai garkuwa da ake zargin yana cikin ƙungiyar masu satar mutane da ke adabar mutane a ƙananan hukumomin Batsari, Safana, Ɗan Musa da Kurfi a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel