An yi garkuwa da Alkalan kotun Shari'ar Musulunci biyu a Najeriya

An yi garkuwa da Alkalan kotun Shari'ar Musulunci biyu a Najeriya

- Garkuwa da mutane ya zama ruwa dare a Arewacin Najeriya

- Kusan kullin sai an sace mutane don karban kudin fansa musamman a Arewa maso yamma

An yi awon gaba da wasu Alkalan kotun Shari'ar Musulunci biyu yan jihar Zamfara yayinda suke hanyar dawowa daga jamhurriyar Nijar ranar Juma'a, 11 ga Satumba, Premium Times ta ruwaito.

An sace Alkalan, Sheikh Sabiu Abdullahi da Sheikh Shafi'i Jangebe, ne yayinda suke hanyarsu ta komawa Zamfara bayan halartan wani taro da suka yi a Nijar.

Malam Sabi'u Abdullahi ne na'ibin limanin Masallacin Juma'an Usaimin dake Gusau.

Abokinsa, babban limanin Masallacin Umar bin Khaddab dake Gusau, Sheikh Umar Kanoma, ya tabbatar da hakan a hudubar Juma'a.

"Muna baran addu'a daga al'ummar Musulmi kan Alkalai biyu da aka sace yayinda suke hanyar dawowa daga Maradi a jamhurriyar Nijar," Yace.

Limamin ya yi kira da gwamnatoci su kare rayukan mutane da dukiyarsu.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Muhammad Shehu, bai amsa kiran waya da sakonnin da aka tura masa ba.

KU KARANTA WANNAN: Yari makaryaci ne, ban zabawa Matawalle kwamishanoni ba - Marafa

An yi garkuwa da Alkalan kotun Shari'ar Musulunci biyu a Najeriya
An yi garkuwa da Alkalan kotun Shari'ar Musulunci biyu a Najeriya
Asali: UGC

An bangare guda, wani kasurgumin dan fashi kuma mai garkuwa da mutane da ya addabi jihar Rivers, Honest Digbara wanda aka fi sani da Bobisky, ya gamu da ajalinsa hannun jami'an hukumar yan sanda.

An bindige dan bindigan wanda aka dade ana nema ruwa a jallo ne ranar Asabar. Al'ummar jihar sun shiga murna da farin ciki yayinda suka samu labarin mutuwan Bobisky.

DUBA NAN: Malamin sakandare ya lalata dalibarsa mai rubuta jarabawar WAEC

Gabanin samun nasarar hallakashi, gwamnati ta yi alkawarin kudi milyan 30 ga duk wanda ya ke da labarin inda dan bindiga yake.

An damke shine a wani harin bazata da hukumar yan sandan Rivers ta kai garin Korokoro dake karamar hukumar Tai ta jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel