Bidiyo: An tilasta wa ɓarawon kaza cin ɗanyen kazar da aka kama shi ya sata

Bidiyo: An tilasta wa ɓarawon kaza cin ɗanyen kazar da aka kama shi ya sata

- Fusatattun matasa sun yi wa wani barawon kaza hukunci Mai tsauri bayan kama shi da kaza a cikin rigarsa

- Matasan sun tilasta masa cin ɗanyen kazan tunda a cewarsu dama ya sace kazan ne domin ya ci

- Mutumin ya yi ƙoƙari ya fara cin ɗanyen kazar amma ya fara amai tun ma bai yi nisa ba

Wasu fusatattun matasa a kasar Zimbabwe sun yi wa wani barawon kaza hukunci nan take bayan kama shi dumu-dumu yana satar kaza.

Asirin mutum ya tonu ne a lokacin da kazar da ya boye a cikin rigarsa ta rika ihun sakamakon matsin da ta ke ciki.

DUBA WANNAN: Bidiyo: Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Goron-Dutse

Fusatattun matasa sun taru sun kuma tilasta masa cin naman ɗanyen kazar a matsayin hukunci.

Ana iya cin muryar wani a cikin bidiyon yana cewa ya fara cin kazan kawai tunda dama ya yi satar ne da niyyar cin kazan.

Kamar yadda ya ke cikin bidiyon, ana iya ganin mutum yana tauna kan kazar.

Savanna News ta ruwaito cewa mutumin ya fara amai bayan ya cinye kan kazar.

Ga dai bidiyon a ƙasa:

KU KARANTA An kama wani da yayi shekaru 2 yana karbar albashin kwamishina a Niger Read

A wani rahoton, kun ji cewa Rundunar Ƴan sandan jihar Katsina sun kama wani hatsabibin mai garkuwa da mutane, Abubakar Ibrahim a dajin Rugu da ke jihar.

An kuma ceto mutum uku da ya yi garkuwa da su bayan kama mai garkuwa da ake zargin yana cikin ƙungiyar masu satar mutane da ke adabar mutane a ƙananan hukumomin Batsari, Safana, Ɗan Musa da Kurfi a jihar.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Gambo Isah ne ya bayar da wannan sanarwar kamar yadda LIB ya ruwaito.

Kakakin ya kuma ce wanda aka kama ɗin ya bayyana cewa shine ya yi wa wasu ƴan bindiga jagoranci a ranar 7 ga watan Satumba suka kai hari a ƙauyukan Dagarawa da Kudewa a ƙananan hukumomin Safana da Kurfi a jihar.

An kuma kwato kuɗin fansa N241,000 da ya karba bayan sace su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164