Ortom ya bukaci sojoji su saki 'yaran' Gana su 40 bayan kashe shugabansu

Ortom ya bukaci sojoji su saki 'yaran' Gana su 40 bayan kashe shugabansu

- Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya buƙaci rundunar soji ta sako ƴan daba 40 da ke yi wa Gana aiki

- Hakan ne zuwa ne bayan rundunar soji ta ce Gana ya mutu sakamakon arangama tsakaninsa da sojoji

- Ortom ya kuma ce gwamnatinsa za ta yi aiki tare da soji da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da hakan bai sake faruwa ba

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom bukaci rundunar sojojin Najeriya ta saki ƴan daba guda 40 da suke tsare da su bayan kashe shugabansu Terwase Akwaza da aka fi sani da Gana.

Gwamnan ya yi wannan kirar ne bayan taron tsaro da aka yi a gidan gwamnati a Makurdi na tsawon awa biyar a ranar Juma'a 11 ga watan Satumba.

Ortom ya bukaci sojoji su saki yaran Gana su 40 bayan kashe shugabansu

Ortom ya bukaci sojoji su saki yaran Gana su 40 bayan kashe shugabansu. Hoto daga LIB
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kayayyakin abinci sun yi sauki a kasuwannin Najeriya, in ji Garba Shehu

Ortom ya ce yana kira a saki tubabbun yan daban ne domin su rungumi shirin afuwa da gwamnatin jihar ta ɓullo da shi.

Ya ce;

"Bayan taro, majalisar tsaro na jihar ta cimma matsayar cewa a sako tubabbun ƴan daban da ke hannun sojoji domin su rungumi shirin afuwa na gwamnati da ke suke hanyar zuwa yayin da aka kama su.

"Kazalika, muna kira a dawo mana da dukkan kayayyakin da aka kama tare da su. Wasu daga cikin motoccin na haya ne, wasu na ma'aikatan gwamnatin mu ne. Wasu takardun kuma na gwamnati ne."

A kan mutuwar Gana, Ortom ya ce mutanen Sankara da na jihar ba su ji dadin abinda ya faru ba.

Ya cigaba da cewa babu yadda za a dawo da wanda ya mutu amma gwamnatin jihar za ta yi aiki tare da sojojin domin gano dalilin mutuwarsa.

KU KARANTA: Bidiyo: Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Goron-Dutse

Ortom ya ce;

"Zamu gano gaskiyan abinda ya faru. Wannan shine abinda kowa ke son ya sani domin rahotanni da muka samu daga kafafen watsa labarai ba su gamsar da mu ba.

"Mun yanke shawarar aiki tare da rundunar soji da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa hakan bai sake faruwa ba."

A wani rahoton da Legit.ng Hausa ta wallafa, Rundunar Ƴan sandan jihar Katsina sun kama wani hatsabibin mai garkuwa da mutane, Abubakar Ibrahim a dajin Rugu da ke jihar.

An kuma ceto mutum uku da ya yi garkuwa da su bayan kama mai garkuwa da ake zargin yana cikin ƙungiyar masu satar mutane da ke adabar mutane a ƙananan hukumomin Batsari, Safana, Ɗan Musa da Kurfi a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel