Zamu raba yan sabbin dogayen motocin sufuri 2000 domin rage radadin hauhawar farashin mai - Gwamnatin Buhari

Zamu raba yan sabbin dogayen motocin sufuri 2000 domin rage radadin hauhawar farashin mai - Gwamnatin Buhari

- Shugaba Buhari zai fitar da hanyar ragewa yan Najeriya radadin tashin farashin man fetur

- An kara farashin litan mai daga N148 zuwa N162 a watan Satumba

- Shugaba Buhari ya ce Najeriya ba zata sake biyan kudin tallafin mai ba

Gwamnatin tarayya a ranar Juma'a ta bayyana cewa ta kammala shirin raba motoci 2000 domin sufuri a fadin tarayya domin rage radadin tashin farashin man fetur kan yan Najeriya musamman masu zama a karkara.

Ministan harkoki na musamman, George Akume, ya bayyana hakan a Abuja a taron tattaunawar da yayi da yan kungiyoyin hadaka.

A cewarsa, shirin zai gudana ne tsakanin ma'aikatarsa, ma'aikatar aikin noma da raya karkara da kuma wasu hukumomin gwamnati.

Akume ya ce an yanke shawarar bi ta hannun kungiyoyin hadaka ne saboda tabbatar da aiwatar da shirin, maimakon baiwa wasu daidaikun mutane bashi, wanda hakan zai jinkirta aiwatar da aikin.

"Abinda muka lura shine, idan aka baiwa daidaikun mutane bashi, dawowa da shi na matukar wuya, amma idan akayi da kungiyoyin hadaka, abin zai fi saukin lura." Akume yace

"Manufar wannan shiri shine tabbatar da cewa mutanen karkara na samun saukin sufuri, yanzu da aka samu tashin farashin man fetur."

"Muna sane da cewa wasu yan kasuwan motocin haya zasu kara farashin hawa mota."

"Amma idan muka aiwatar da wannan shiri, mun yi imanin cewa zai rage tashin farashin don jin dadin al'ummarmu."

Ya ce babu yadda kasar nan zata cigaba ba tare da Sufuri ba wanda shine dalilin da yasa shugaba Muhammadu Buhari ke aiki tukuru ta bangaren gyaran hanyoyi, jiragen kasa da na sama.

KU KARANTA: Ambaliya a jihar Bauchi: Mutane 16 sun mutu, gidaje 2000 sun salwanta

Zamu rabawa yan sabbin dogayen motocin sufuri 2000 domin rage radadin hauhawar farashin mai - Gwamnatin Buhari

Gwamnatin Buhari
Source: Twitter

A bangare guda, PPRA, hukumar gwamnatin tarayya da ke da alhakin kayyade farashin albarkatun man fetur, ta ce daga yanzu babu ruwanta da maganar tsayar da farashin mai, magana ta koma hannun 'yan kasuwa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa babban sakataren hukumar PPRA, Abdulkadir Saidu, ne ya sanar da hakan.

A cewar jaridar Punch, Saidu ya bayyana cewa daga yanzu kayyade farashin litar mai zai dogara ne a kan bukatarsa da kuma farashin danyen mai a kauwar duniya.

Hakan na nufin gwamnati ta tsame hannunta daga tsayarwa ko kayyade farashin litar mai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel