Jerin sunaye: Buhari ya yi sabbin nade-nade a bangaren wutar lantarki

Jerin sunaye: Buhari ya yi sabbin nade-nade a bangaren wutar lantarki

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon kwamiti a fannin wutar lantarki

- Mambobin sabon kwamitin sun hada da Babatunde Fashola, Abubakar Malami da sauransu

- Kwamitin zai mayar da hankali wurin tabbatar da cikar burin Buhari wurin inganta wutar lantarki

Daga cikin kokarin tabbatar da ingancin a fannin wutar lantarki a fadin kasar nan, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wasu manya daga makusantansa a cikin kwamitin inganta wutar lantarki na shugaban kasa (SPVPPI).

Shugaban kasar ya amince da sabbin nade-naden a ranar Alhamis, 10 ga watan Satumban 2020 kamar yadda yake kunshe a wata takarda da ta fito daga ofishin ma'aikatar shari'a.

Mambobin kwamitin sun hada da antoni janar na tarayya, Abubakar Malami (SAN) da ministan kudi, kasafi da tsari, Hajia Zainab Ahmed .

Buhari ya kara da nada ministan wutar lantarki, Saleh Mamman da ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, duk a cikin mambobin kwamitin na musamman.

Mai magana da yawun Malami, Umar Gwandu, wanda ya saki takardar, ya bayyana cewa sauran mambobin sun hada da darakta janar na NBPE, Alex Okoh da Babagana Mohammed, shugaban kungiyar injiniyoyi ta Najeriya.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Matar mataimakin gwamna na zargin Adams Oshiomhole da yi mata barazanar kisa

Jerin sunaye: Buhari ya yi sabbin nade-nade a bangaren wutar lantarki

Jerin sunaye: Buhari ya yi sabbin nade-nade a bangaren wutar lantarki. Hoto daga Vanguard
Source: UGC

KU KARANTA: Sai muna kwance ni da ita sai ta sulale zuwa dakin wani gardi suyi iskanci - Malamin Islamiyya ya kai matar shi kara kotu

A yayin rantsar da kwamitin a ranar Alhamis, shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya kwatanta sashin wutar lantarki a matsayin fanni mai matukar amfani, ya bayyana cewa zai jajirce wurin tabbatar da cewa matsalar wutar lantarki ta zama tarihi.

A wani labari na daban, Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 11 ga watan Augusta, ya nada Adamu Adaji a matsayin darakta janar na NBC.

Kamar yadda takaradar da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya saka hannu, nadin Adaji ya fara aiki daga ranar Juma'a, 7 ga watan Augustan 2020.

Shugaban fannin yada labarai na NBC, Ovuakporie Efe, ya bayyana cewa wannan sabon nadin da aka yi wa shugaban zai kwashe shekaru hudu a wannan kujerar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel