Na kan sha fitsarin shanu a kullum don kiyayye kamuwa daga cutar korona - Akshay Kumar

Na kan sha fitsarin shanu a kullum don kiyayye kamuwa daga cutar korona - Akshay Kumar

- Fitaccen Jarumin Bollywood Akshay Kumar ya bayyana cewa a kullum ya kan sha fitsarin shanu don maganin korona

- Kumar ya sanar da hakan ne a dandalin sada zumunta bayan ya sha shayin da aka haɗa da kashin giwa tare da wani mutumin Ingila a talabijin

- Mabiya addinin Hindu da dama a Indiya suna ganin shanu dabba ce mai karama kuma abinda ke fita daga jikin ta na magunguna

Jarumin Bollywood Akshay Kumar ya bayyana cewa a kullum ya kan sha fitsarin shanu domin kiyayye kansa daga kamuwa daga cutar korona.

Jarumin ya shiga sahun mutane da dama a Indiya da suka yi imanin cewa fitsarin shanun na maganin Coronavirus.

Na kan sha fitsarin shanu a kullum don kiyayye kamuwa daga cutar korona - Akshay Kumar

Na kan sha fitsarin shanu a kullum don kiyayye kamuwa daga cutar korona - Akshay Kumar. Hpto daga Daily Trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa ƴar Sanata Wamakko rasuwa a Sokoto

Ana yi wa Kumar kallon magoyin bayan jam'iyyar masu kishin Hindu na Farai Minista Narendra Modi wacce ta ware miliyoyin daloli domin bincike kan amfani da fitsari da bayan gidan shanu wurin yin magungunan ciwo kamar ciwon suga da na daji.

Babu wani sahihin hujja a kimiyyance da ke nuna fitsari ko kashin shanu na magani amma yan siyasa da dama daga jam'iyyar Modi suna iƙirarin amfani da shi wurin maganin coronavirus.

Jarumin mai shekaru 53 yana tallata wani sabon shirinsa ne tare da wani baturen Ingila Bear Grylls inda suka sha shayi da aka haɗa da kashin giwa a wani wurin ajiye damisa a Indiya.

"Ba na damuwa ko kaɗan. Ina shan fitsarin shanu kullum saboda amfanin sa ga lafiya saboda haka babu matsala," Kumar ya wallafa a dandalin sada zumunta a ranar Alhamis.

Mabiya addinin Hindu da dama sunyi imanin shanu na da wata karama ta musamman kuma su kan sha fitsarin shanun domin magunguna.

KU KARANTA: Bidiyo: Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Goron-Dutse

Gwamnatin Modi ta kafa Ma'aikata na magungunan gargajiya ta 'ayurveda' da motsa jiki wato 'yoga'.

Farai Ministan ya nuna cewa yoga na iya taimakawa wurin kare kai daga kamuwa daga cutar korona.

Mutum miliyan 4.6 ne suka kamu da Covid-19 a Indiya kuma cutar ta kashe mutane 76,000.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa kun ji gwamnatin jihar Abia ta ce ta gano bullar cutar tarin tuberculosis (TB) na shanu a jihar hakan yasa ta gargadi mazauna jihar su dena cin huhun shanu.

Kwamishinan noma na jihar, Ikechi Mgboji ne ya sanar da hakan a ranar Talata 8 ga watan Satumba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel