Wasu yan iska na shirya yadda wani tsohon gwamna zai gaji Buhari - Kabiru Marafa

Wasu yan iska na shirya yadda wani tsohon gwamna zai gaji Buhari - Kabiru Marafa

- Sanata Kabir Marafa ya yi martani mai zafi ga tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari

- Tsohon dan majalisan na jagorantan daya daga cikin ballin jam'iyyar APC a jihar Zamfara

- Marafa ya yi tsokaci kan shirin da wasu gwamnonin APC ke yi na daura dan Arewa kujerar Buhari a 2023

Sanata Kabiru Marafa ya yi martani kan kalaman tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari cewa sun shirya dinke barakar gida da ta ruguza jam'iyyar APC a jihar a shekarar 2019.

Yari ya yi jawabi kan shirin da shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, ke yi na haduwa da masu ruwa da tsaki a jihar Zamfara don shirya tsakaninsu.

DUBA NAN: Kisan Gana: Maimakon sukanmu, milyan 50 da kayi alkawari za ka bamu - Hukumar Soji

A hirar da Sanata Marafa yayi ranar Alhamis, 10 ga Satumba, yace: "Ban yi mamakin kalaman dake fita daga bakin Yari ba kuma ko a jikina. Idan yace babu baraka cikin jam'iyyar APC a Zamfara, na yarda, mu jira zagaye na biyu."

Yayin tsokaci kan shirin da gwamna Mai Mala Buni ke yi na dinke barakar jam'iyyar, Marafa yace: "Abinda na sani shine kwamitin tun yanzu tana tafka kura-kurai saboda tana sauraron irinsu Yari masu baki biyu."

"Akwai yan tsirarun mutanen kirki a kwamiti dake nufin jam'iyyar da alkhairi kuma ina mai basu shawara su tashi tsaye suyi abinda aka umurcesu su ajiye siyasar 2023. Babu wanda zai iya kawo kujerar shugaban uwar jam'iyya Arewa yanzu."

"Shirin da wasu yan iska keyi cikin gwamnoni na kwace jam'iyyar ta hanyar daura wani gwamna mai ci sannan zaben wani tsohon gwamna ya gaji Buhari zai fadi warwas kamar yadda shirin Yari ya ruguje gaba daya."

KU KARANTA: Na'urar 'Card Reader' 5000 mukayi asara a gobarar jiya - Hukumar INEC

Wasu yan iska na shirya yadda wani tsohon gwamna zai gaji Buhari - Kabiru Marafa

Wasu yan iska na shirya yadda wani tsohon gwamna zai gaji Buhari - Kabiru Marafa
Source: Facebook

A ranar 8 ga Satumba, mun kawo muku rahoton cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Abubakar Yari, ya bayyana cewa mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar sun shirya yin sulhun gaske yanzu bayan rikicin cikin gida tsakaninsa da Sanata Kabiru Marafa.

Bangaren Kabiru Marafa da na Yari sun kasance cikin bakin kiyayya tun gabanin zaben 2019.

Yari ya jagoranci tawagar mambobin jam'iyyar zuwa wajen shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, a Sakatariyar jam'iyyar dake Abuja.

Ya bayyana dalilan da ya sa ake bukatar sulhu a jihar, kuma ya ce dukkan abokan hamayya su gabato da niyya mai kyau.

Amma Yari yace matsalan shine wasu daga cikin mabiya Sanata Kabiru Marafa tuni sun hada kai da gwamnatin Bello Matawalle na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel