Allah ya yi wa ƴar Sanata Wamakko rasuwa a Sokoto

Allah ya yi wa ƴar Sanata Wamakko rasuwa a Sokoto

- Ɗiyar tsohon gwamnan Sokoto, Aliyu Magatakarda Wamakko, Sadiya Wammako ta rasu

- Sadiya ta rasu ne a ranar Alhamis 10 ga watan Satumba a asibitin koyarwa na jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto

- An yi jana'izar marigayiyan a gidan Sanata Wamakko da ke Sahabi Dange Road, Gawon Nama a Sokoto

Allah ya yi wa ƴar Sanata Wamakko rasuwa a Sokoto
Allah ya yi wa ƴar Sanata Wamakko rasuwa a Sokoto. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi rashin yarsa Sadiya Magatakarda Wamakko da ta rasu a ranar Alhamis 10 ga watan Satumban 2020.

Sadiya ta rasu ne a asibitin koyarwa ta jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto a lokacin da ta tafi asibitin don haihuwa.

Marigayiya Sadiya ta rasu tana da shekaru 23 a duniya.

DUBA WANNAN: An kama wani mutum dauke da katin ATM 2,886 a filin jirgin sama zai tafi Dubai (Hotuna)

An yi jana'izar ta a daren ranar Alhamis, 10 ga watan Satumba a gidan Sanata Wamakko da ke Sahabi Dange Road, Gawon Nama a Sokoto.

Babban limamin masallacin Juma'a ta Sultan Bello a Sokoto, Liman Malami Shehu Akwara ne ya yi limancin sallar jana'izar kamar yadda LIB ta ruwaito.

Tsohon gwamnan shine shugaban kwamitin tsaro kuma mataimakin shugaban kwamitin yaki da rashawa a majalisar dattawa.

Allah ya jikan ta da raham. Amin.

Ga hotunan sallar jana'izar ta a ƙasa.

Allah ya yi wa ƴar Sanata Wamakko rasuwa a Sokoto
Allah ya yi wa ƴar Sanata Wamakko rasuwa a Sokoto. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

Allah ya yi wa ƴar Sanata Wamakko rasuwa a Sokoto
Allah ya yi wa ƴar Sanata Wamakko rasuwa a Sokoto. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo: Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Goron-Dutse

Allah ya yi wa ƴar Sanata Wamakko rasuwa a Sokoto
Allah ya yi wa ƴar Sanata Wamakko rasuwa a Sokoto. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa kun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya kafa wata kwamiti da za ta cigaba da jan ragamar bunkasa tattalin arzikin ƙasar mai suna Agenda 2050.

Wannan kwamitin za ta ɗora ne a kan tsarin tattalin arziki na vision 2020 da tsohon shugaban kasar Musa Yar'adua ya kaddamar da wasu tsare tsaren.

Ɗan kasuwa Mista Atedo Peterside da ministan kuɗi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed ne za su jagoranci kwamitin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mashawarcin shugaban kasa na musamman, Femi Adesina ya bayyana hakan cikin wata sanarwa mai taken "Agenda 2050: Shugaba Buhari ya kafa kwamitin jagorancin ƙasa da za ta yi aiki don tsamo ƴan Najeriya miliyan 100 daga talauci zuwa shekarar 2030."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel