Na'urar 'Card Reader' 5000 mukayi asara a gobarar jiya - Hukumar INEC

Na'urar 'Card Reader' 5000 mukayi asara a gobarar jiya - Hukumar INEC

Ofishin hukumar gudanar da zaben kasa mai zaman kanta INEC dake Akure, birnin jihar Ondo na ci bal-bal a daren jiya Alhamis, 10 ga watan Satumba, 2020.

Wannan gobara na zuwa ne saura wata daya zaben gwamnan jihar da aka shirya ranar 10 ga watan Oktoba, 2020.

A jawabin da kakakin hukumar, Barista Festus Okoye, ya saki, ya ce wutar ta kona kwantenan da aka ajiye na'u'rorin Card Reader.

"Ko kafin yanzu mun ajiye na'urar 'Card Reader' 4000 cikin kwantenan amma an kara 1000 domin zaben da ake shiri a jihar." Okoye yace

"Saboda haka muna da 'Card Reader' 5100 da gobarar ta lashe."

Ya tabbatar da cewa ba'ayi rashin rai da jin rauni ba amma ya ki bayyana abinda ya haddasa gobarar.

KU DUBA WANNAN: Sojoji sun hallaka kasurgumin dan bindigan jihar Benue, Terwase Gana

Na'urar 'Card Reader' 5000 mukayi asara a gobarar jiya - Hukumar INEC
Na'urar 'Card Reader' 5000 mukayi asara a gobarar jiya - Hukumar INEC
Asali: Twitter

A jiya da gobarar ta faru, Festus Okoye yace za'a kaddamar da bincike ba tare da bata lokaci ba idan aka kammala kashe wutar.

Yace: "Gobara ta barke , Alhamis, 10 ga Satumba, 2020 a hedkwatar hukumar INEC dake Akure. Wutar ta kona kwantenan da aka ajiye na'urorin Card Reader misalin karfe 7:30 na dare."

"Yanzu haka jami'an kwana-kwana na kokarin kashe wutar."

"Kwamishanan yada labarai na hukumar, Festus Okoye, wanda yake jihar Ondo yanzu domin shirye-shiryen zaben da aka shirya yi ranar 10 ga watan Oktoba, 2020 ya garzaya ofishin misalin karfe 8."

DUBA NAN: Mun ceto mutane 5 cikin wadanda aka sace a Abuja cikin daren Laraba - Yan sanda

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel