Kisan Gana: Maimakon sukanmu, milyan 50 da kayi alkawari za ka bamu - Hukumar Soji

Kisan Gana: Maimakon sukanmu, milyan 50 da kayi alkawari za ka bamu - Hukumar Soji

- Maimakon cacan baki, Sojoji sunce kudi suke bukata daga gwamna Ortom

- Sojojin rundunar Special Forces sun bindige dan ta'adda, Terwase Gana, ranar Talata

- Babban hafsan Soji, Tukur Buratai, ya ce ba zai ce komai kan lamarin ba

Hukumar Sojin Najeriya ta na bukatar alkawarin milyan hamsin da gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya yiwa duk wanda ya kama shahararren kasugurmin dan bindiga, Terwase Agwaza (a.k.a Gana)

Wannan bukata na zuwa ne bayan kwanaki uku da jami'an rundunar Special Forces Command dake Doma, jihar Nasarawa suka hallaka dan bindigan.

Wata majiya mai siqa a gidan Soja, ta bayyanawa jaridar The Nation cewa hukumar na jiran tsammani ko gwamnan zai cika alkawarinsa.

Majiyar tace idan ya cika alkawarin, hakan zai nuna irin goyon bayan da yan siyasa ke yiwa hukumar Soja.

DUBA NAN: Sojoji sun hallaka kasurgumin dan bindigan jihar Benue, Terwase Gana

A cewar Majiyar: "Jami'an Special Forces sun kawar da kasurgumin dan bindiga kuma dan ta'adda, Terwase Agwaza, wanda ya dade yana addabar jihar Benue da kewaye. Ya kasance cikin wadanda jami'an tsaro ke nema ruwa a jallo."

"Jami'an Sojin Special Forces sun kai wani hari na musamman inda suka wargaza sansanin yan ta'addan da suka addabi yan Najeriya a hanyar Nasarawa zuwa Kogi kwanakin nan."

"Gwamnan jihar Benue ya yi alkawarin milyan 10 ga duk wanda ya bada bayanin inda za'a kama Gana"

"Amma duk da haka ba'a samu damar kamashi ba. Daga baya gwamna ya kara kudin zuwa milyan hamsin, duk da haka an gaza kamashi, sai ranar 8 ga Satumba, 2020 da Sojojin Special Forces suka bindigeshi."

"Saboda haka, hukumar Soji ta cancanci a biyata N50 million, tun da an kashe Gana."

Sau uku gwamna Samuel Ortom yana alkawarin kudi ga duk wanda ya bada bayani kan Gana. Daga milyan 5, zuwa 10 a shekarar 2017, sannan milyan 50 a Yulin 2020.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Matar mataimakin gwamna na zargin Adams Oshiomhole da yi mata barazanar kisa

Kisan Gana: Maimakon sukanmu, milyan 50 da akayi alkawari za ka bamu - Hukumar Soji
Kisan Gana: Maimakon sukanmu, milyan 50 da akayi alkawari za ka bamu - Hukumar Soji
Asali: UGC

Dubun Shahrarren dan bindigan da aka dade ana nema ruwa a jallo, Terwase Agwaza Gana, ya cika hannun jami'an Sojin 'Special forces' a ranar Talata, 8 ga Satumba, 2020.

Kwamandan 4 Special Forces Command, Doma, jihar Nasarawa, Maj. -Gen. Moundhey Ali, ya bayyanawa manema labarai ranar Laraba cewa an kashe Gana ne a hanyar Gbese-Gboko-Makurdi bayan musayar wuta.

Yace, "Misalin karfe 12:00 na ranar Talata, mun samu labarin shahrarren dan bindiga Terwase Akwaza Agbadu wanda aka fi sani da Gana na hanyar Gbese-Gboko-Makurdi.

"Misalin karfe 13:00, an yi musayar wuta tsakanin Soji da Gana inda aka kasheshi."

Kwamandan ya ce an damke yaran aikinsa 40 da manyan makamai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel