Yanzu-yanzu: Likitocin Najeriya sun janye yajin aiki, zasu koma bakin aiki

Yanzu-yanzu: Likitocin Najeriya sun janye yajin aiki, zasu koma bakin aiki

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa a Najeriya NARD ta dakatad da yajin aikin da ta tafi sakamakon rashin cimma matsaya da gwamnatin tarayya da kudaden alawus din mambobinta.

Shugaban kungiyar, Dr Aliyu Sokomba, ya tabbatar da hakan ga tsahar Channels da yammacin Alhamis.

Sokomba ya bayyana cewa kungiyar za ta cigaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya bayan makonni biyu.

A ranar Laraba, gwamnatin tarayya da Likitoci sun cimma matsaya domin kawo karshen yajin aikin.

A ganawar da aka kwashe kwana daya ana yi, wakilan likitocin sun bayyana cewa zasu tattauna da majalisar zartaswar kungiyar domin ganin yiwuwar janye yajin aikin.

Bayan zaman ranar Laraba, gwamnatin tarayya ta ce zata kara musu N8.9 billion matsayin kudin alawus na COVID19 na watan Yuni ga dukkan Likitocin Najeriya.

Ministan Kwadago, Sanata Chris Ngige, ya bayyana haka yayin rattafa hannu kan takardar yarjejeniyar da aka yi.

Ngige ya ce an kammala shirin biyan kudin kuma tuni an turawa babbar bankin Najeriya CBN takarda ta fara biya daga ranar 9 ga Satumba.

A cewarsa, jimillan kudin da aka biyasu yanzu ya kai N288 billion.

DUBA NAN: Macijiya ta gantsari matashi a azzakari sai da ya kusa bakuntan lahira

Yanzu-yanzu: Likitocin Najeriya sun janye yajin aiki, zasu koma bakin aiki
Yanzu-yanzu: Likitocin Najeriya sun janye yajin aiki, zasu koma bakin aiki
Source: Twitter

Kafin samun nasarar cimma matsaya, gwamnatin tarayya ta umarci shugabanni asibitoci na tarayya da su gaggauta fara amfani da manyan likitoci da kuma masu hidimar kasa domin maye gurbin likitocin da suka tafi yajin aiki.

Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya bada wannan umarnin a wata takarda da ya fitar a garin Abuja a ranar Laraba, jaridar The Punch ta wallafa.

Yana yin martani ne game da yajin aikin da kungiyar likitoci masu neman kwarewa suka yi a kan rashin biyansu alawus na hatsarin Covid-19 da sauran bukatunsu.

Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar NARD ta likitocin da ke neman kwarewa a aiki ta ce yajin da ta daka ya soma aiki ne a ranar au Litinin, 7 ga watan Satumba, 2020.

Likitocin asibitocin kasar sun tafi yajin aiki a sakamakon gaza zama da shugabanninsu da gwamnatin tarayya ta yi a ‘yan kwanakin bayan nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel