Hotuna: Magoya bayan APC sun ragargza shagunan wasu 'yan kasuwa da suka koma PDP

Hotuna: Magoya bayan APC sun ragargza shagunan wasu 'yan kasuwa da suka koma PDP

- Wasu magoya bayan jam'iyyar APC a jihar Yobe sun shiga kasuwa inda suka ragargaza shagunan wasu 'yan kasuwa

- An gano hakan ta faru ne bayan da suka zargi 'yan kasuwar da sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP

- Kamar yadda ganau ba jiyau ba suka sanar, sun ce har da 'yan sandan Hisbah aka yi wannan ragargazar

Wasu magoya bayan jam'iyyar APC tare da hadin guiwar jami'an hukumar Hisbah ta jihar Yobe, sun ragargaza shagunan wasu 'yan kasuwa, wadanda suka sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a garinsu Gwamna Mai Mala Buni.

Wannan ragargazar ta faru ne kasa da sa'o'i 24 bayan 'yan kasuwar sun koma jam'iyyar PDP daga APC.

Wani ganau ba jiyau ba, ya sanar da Sahara Reporters cewa 'yan sandan Hisbah sun bada babbar gudumawa wurin ragargaza shagunan.

Sun ce sun bude shafin rigima da duk wanda ya bar jam'iyyar APC kuma ya koma PDP a jihar.

Hotuna: Magoya bayan APC sun ragargza shagunan wasu 'yan kasuwa da suka koma PDP
Hotuna: Magoya bayan APC sun ragargza shagunan wasu 'yan kasuwa da suka koma PDP. Hoto daga Sahara Reporters
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon wani yaro da yake yiwa mahaifiyarshi bayanin yadda ya kamu da son wata budurwa ya bawa mutane mamaki

Hotuna: Magoya bayan APC sun ragargza shagunan wasu 'yan kasuwa da suka koma PDP
Hotuna: Magoya bayan APC sun ragargza shagunan wasu 'yan kasuwa da suka koma PDP. Hoto daga Sahara Reporters
Asali: Twitter

Hotuna: Magoya bayan APC sun ragargza shagunan wasu 'yan kasuwa da suka koma PDP
Hotuna: Magoya bayan APC sun ragargza shagunan wasu 'yan kasuwa da suka koma PDP. Hoto daga Sahara Reporters
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tirkashi: An dakatar da daurin aure bayan wani mutumi ya shiga wajen daurin aure yace shine mahaifin amarya da ango

A wani labari na daban, jami'an rundunar 'yan sanda sun kama wasu daga cikin masu zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin man fetur.

An kama masu zanga-zangar ne a yau, Alhamis, a yankin Ojuelegba da ke garin Legas. Jaridar Punch ta rawaito cewa bayan masu zanga-zangar da aka kama, an kwace kayan aikin 'yan jaridu.

Daya daga cikin jagororin masu zanga-zangar, Hassan Soweto, ya ce an kama mutane 18 da suka hada da 'yan jarida.

"An kama mu tare da 'yan jarida da mambobin jam'iyyar SPN da safiyar yau (Alhamis) yayin da muka fito zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin man fetur da kudin wutar lantarki.

"A yanzu haka da nake rubuta wannan sako ina kulle a bayan motar 'yan sanda a hanyar zuwa hedikwatarsu," a cewar Soweto, shugaban matasan SPN.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel