An kama wani mutum dauke da katin ATM 2,886 a filin jirgin sama zai tafi Dubai (Hotuna)

An kama wani mutum dauke da katin ATM 2,886 a filin jirgin sama zai tafi Dubai (Hotuna)

- Jami'an hukumar Kwastam sun kama wani mutum da katin ATM 2,886 da layukan waya hudu a filin jirgin sama

- Mutumin, Ishaq Abubakar ya yi iƙirarin cewa ya fito daga Kano ne kuma zai tafi kasar Dubai

- An gano cewa ya boye katin ATM ɗin da layukan wayan ne a cikin taliyar indomie saboda kar a kamashi

Ofishin hukumar yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta'annati, EFCC, ta fara bincike a kan wani da ake zargin ɗan damfara ne da aka kama ya ɓoye katim ATM 2,886 da layyukan waya hudu cikin taliyar indomie.

Jami'an hukumar Kwastam ne suka mika wanda ake zargin, Ishaq Abubakar ga hukumar EFCC a ranar Alhamis 10 ga watan Satumban 2020 domin a bincike shi.

Katin ATM
Katin ATM
Asali: Twitter

Abubakar ya faɗa cikin matsala ne a lokacin da jami'an Kwastam da ke filin tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas suka kama shi a hanyarsa ta zuwa Dubai dauke da katin ATM 2,886 da layin wuya hudu ɓoye cikin indomie.

A yayin da ya ke mika wanda ake zargin hannun EFCC a Legas ranar Alhamis, mataimakin kwantrola, Abdulmumin Bako ya ce;

"Jami'an Kwastam da ke filin tashin jiragen sama na Murtala Muhammed, a ranar 22 ga watan Agustan 2020 sun kama wanda ake zargin da katin ATM 2,886 da layin waya hudu, da ya boye su da kyau cikin taliyar indomie."

An kama wani matafiyi da ATM 2,886 da layukan waya hudu a filin jirgin sama
An kama wani matafiyi da ATM 2,886 da layukan waya hudu a filin jirgin sama. Hoto daga EFCC
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Jaruman matasa 3 da suka ƙwaci kansu daga hannun masu garkuwa a Katsina sun samu kyauta daga gwamnati

Bako wanda ya samu wakilcin, Area Kwantrola, A. Ma'aji ya ƙara da cewa, "Wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa ya taho daga Kano ne zai tafi Dubai amma aka lura wani yana taya shi wuce wuraren bincike a filin jirgin.

"Hakan ya janyo hankalin jami'an suka ce dole sai sun caje shi sosai bayan na'urar bincike ta nuna yana dauke da taliyar indomie," in ji shi.

An kama wani matafiyi da ATM 2,886 da layukan waya hudu a filin jirgin sama
An kama wani matafiyi da ATM 2,886 da layukan waya hudu a filin jirgin sama. Hoto daga EFCC
Asali: Facebook

A bangarensa, shugaban hukumar EFCC na Legas ya karbi wanda ake zargin a madadin hukumar kuma ya ce za a zurfafa bincike a gano dukkan wadanda ke da hannu cikin lamarin.

KU KARANTA: Bidiyo: An kama wani dumu-dumu yana ƙoƙarin yin zina da matar mai gidansa

A cewarsa, "A madadin hukumar da shugaban riko, Mista Muhammad Umar, mun karbi Ishaq kuma ina tabbatar muku cewa zamu zurfafa bincike mu gano dukkan wadanda ke da hannu."

Ma'aji ya ƙara da cewa akwai alamun laifuka da dama masu alaƙa da almundahana da kuɗi kuma ya ce babu shakka akwai hannun bankuna da masu aikin banki.

An kama wani matafiyi da ATM 2,886 da layukan waya hudu a filin jirgin sama
An kama wani matafiyi da ATM 2,886 da layukan waya hudu a filin jirgin sama. Hoto daga EFCC
Asali: Facebook

Ya ce akwai yiwuwar ba shi kaɗai ya ke aikin ba amma dai za a gudanar da sahihuyar bincike.

A wani rahoton daban, kun ji cewa a ƙalla katon ɗin taliya indomie guda 1,958 cikin 3,850 da ya kamata a raba wa mutane a matsayin tallafi a jihar Benue ne yan sanda suka gano an sayar da su a Kano.

Yan sanda sun yi nasarar kama wadanda ke da hannu wurin karkatar da kayan tallafin, an kuma yi holen su tare da wasu da ake zargi da aikata wasu laifukan a ofishin ƴan sanda ta Bompai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel